Wannan batu ba shi buƙatar wata gabatarwa ko shimfiɗa ballantana wani kewaye-kewaye. Saboda ko mai faskaren itace a daji ya na kaiwa cikin gari, ya na sayarwa, ya san manyan ‘yan boko ne matsalar Najeriya, kuma su ne su ka kashe ta.
Tun daga masu riƙe da manyan muƙamai na siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati na tarayya da jihohi, duk inda ka ji an karkatar da naira biliyan 1 zuwa 5, 10, 50, ko 100 abin da ya yi sama, za ga iske cewa aikin riƙaƙƙun manyan ‘yan boko ne ma’aikatan gwamnatin tarayya ko kuma manyan ‘yan siyasa, kama daga ministoci da gwamnoni da sauran shugabannin cibiyoyi da hukumomin gwamnati.
Babu ƙasar da ta kai Najeriya ƙyanƙyashe manyan ‘yan boko ɓarayi. Sai ka shafe shekaru ka na ilmi, ka zama farfesa a fannin likita, ko ilmin shari’a, fannin tattalin arziki, tarihi, jarida, tasarifin kuɗaɗe, kimiyya da fasaha, injiniya, amma a ƙarshe bayan ka zama shugaba ko jagora, ba za ka amfana wa ƙasar ka ko ƙauyen ku da komai ba, sai ka rikiɗe ka zama tantangaryar ɓarawo.
Ka rayu a Najeriya a banza, za ka mutu a banza, bayan ka mori kuɗin gwamnati an ilmantar da kai, an ciyar da kai ka na kan mulki, bayan ka sauka kuma a ci gaba da kashe kuɗi wajen biyan jami’an EFCC da ICPC su na binciken ka a matsayin ɓarawo. Sannan kuma a ci gaba da kashe wa alƙalai kuɗaɗe su na zaman shari’ar ka a matsayin riƙaƙƙen masani, amma kuma riƙaƙƙen ɓarawo.
Babu macuta irin manyan ‘yan bokon Najeriya, waɗanda su ka sace kuɗaɗen al’umma. To ina banda cuta, ya za ka kwashe kuɗaɗen jama’a tafi Turai da irin su Dubai ka sayi kadarori, ka kimshe kuɗaɗe daga kai sai ‘ya’yan ka. Sannan saboda ka raina wa ‘yan Chana da Turawa hankali, sai ka riƙa bin su wai ka na so su shigo ƙasar ka don ka na Minista ko Gwamna, ka ce su O su zuba jarin bunƙasa ƙasa.
‘Yan siyasa da ‘yan boko masu riƙe da manyan muƙamai duk an yi zaune ana jiran ‘kudaden banza’ daga fetur ɗin da ake haƙowa. A raba kowa ya samu, amma maimakon a taskance su a yi wa al’umma aiki, a bunƙasa ƙasa, a ƙarshe sai ka ji biliyoyin nairori na salwanta a jihohi da ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnati.
Har yanzu iyakar gejin malejin fasaha da kimiyyar mu ba ta wuce maganar shinkafa masarar da ake ci a kasayas ba.
Ina amfanin manyan ‘yan bokon shugabannin Najeriya, a ce duk da arzikin da mu ke da shi, amma tace man fetur ya gagare mu a ƙasar nan?
A manyan kotunan mu shari’u ne jibge na zargin satar biliyoyin kuɗaɗe da gaggan ‘yan boko da ‘yan siyasa su ka yi.
Duk wani ilmin su da sanin dabarar siyasar su, arankatakaf ya ƙare wajen cutar talakawa. Mutanen da su ka cinye kuɗaɗen harkokin inganta lafiya, tsaro, ilmi da tallafin marasa galihu, ai kuɗin da ke hannun mutuwa ne kaɗai ba su iya fizga su ci.
A Abuja dai babu wani sahihin kasuwancin da ake hada-hadar da ke jawo kuɗaɗen da ake kashewa a kullum a cikin birnin. Kai da gani ka san duk kuɗaɗe ne akasari da ke fitowa daga aljifan masu madafun iko da manyan ‘yan kwangilar da ake kashe-mu-raba da su. Su wa ke shirya yadda ake yin kashe-mu-raba idan ba manyan ‘yan bokon da suka haye manyan muƙamai ba.
Talaka shi ya san ya na cikin masifa da takaici da ƙuncin rayuwa. Amma da ya je Abuja zai tabbatar da cewa birni ne wanda kamar babu ba ta taɓa bin hanyar ba.
Super Market da aka gina a Abuja cikin shekaru takwas sun 100. Duk wadda ka shiga da rana, ko da yamma ko da dare, danƙam A ka gan ta da jama’a. Kowa ya lodin abin da ran sa ke so da kuma sauran kayan ci-banza-ci-wofi ana loda, ana miƙa katin ATM ana hada-hadar kuɗaɗe.
A Abuja ba a ma san ana wani abu matsalar ‘yan bindiga a Arewa ba. Kowa harkar sa ya ke yi. Ko zancen ba ka ji ana yi. Sai ɗan abin da ba a rasa ba.
Duk inda ka ga matasa na ragabza, da ka salsalar abin za ka ga daga ɗan wane, sai ƙanen wane, sai jikan wane. Ko kuma ƙanin matar wane.
Kai, a haya kaɗai sai ka samu gidan hayar da kuɗin shekara ɗaya a Abuja zai iya yi wa ƙauyuka birjik rijiyoyin burtsate. Amma sai su shekara 20 babu ruwan balle su samu sassaucin rayuwa.
Najeriya mun fi kowace ƙasa arziki a Afrika. Amma mun fi kowace ƙasa buƙatar taimako daga kungiyoyin bayar da tallafi na ƙasashen Turai.
Idan haka ne wakilcin manyan ‘yan boko a manyan muƙaman gwamnati, to mene ne amfanin karatun bokon na su? Shi ya sa ni ba na kiran su masu ilmi, sai dai ‘yan boko kawai. Saboda sun yi bokoko da babakere kan dukiyar da talakawa ne ya kamata su ci moriyar ta, ba su da iyalan su ba.
Matashiya: Yadda ‘Yan Bokon Najeriya Ke Tauye Haƙƙin Talakawan Ƙasa:
Ɓarawo Ba Shi Da Kama: Yadda Tsohon Shugaban Hukumar NECO Da JAMB Ya Mallaki Kamfanoni, Gidaje Da Ɗimbin Kadarori Daga Naira Biliyan 5.2 ɗin d
Da y
Ya Ɓanƙara a
Aljihu:
A ci gaba da shari’ar tsohon Shugaban Hukumar NECO da JAMB, Dibu Ojerinde da ake yi, wani mai bada shaida wanda Hukumar ICPC ta gabatar a kotu, ya shaida wa Mai Shari’a yadda Ojerinde ya mallaki manyan kamfanoni da maka-makan gidaje, daga cikin naira biliyan ɗin da ake tuhumar su salwanta a hannun sa.
Wannan mai bayar da shaida na farko dai ya fara bayar da shaidar sa, yayin da ƙoƙarin daidaitawa ta hanyar ‘plea bargain’ ba ta yiwu ba.
‘Plea bargain’ shi ne ɓarawon gwamnati ya amince ya saci kuɗin, kuma zai mayar da su. Saboda haka kotu za ta yi masa sassaucin hukunci.
An dai yi ƙoƙarin wannan tattauna batun ‘plea bargain’ a ranar Laraba.
Mai Gabatar da ƙara ya shaida wa Mai Shari’a a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja cewa tsohon Rajistaran JAMB ya mallaki manyan kantama-kantaman kadarori na maka-makan gidaje da kanfanoni a lokacin da ya ke Rajistara na JAMB.
Peter Oyewole, wanda garin su ɗaya da Ojerinde, ya shaida wa kotu cewa ya yi aiki ƙarƙashin Ojerinde a matsayin lauyan sa. Ya ci gaba da bayar da shaida kan abin da ya san Ojerinde ya saya da naira biliyan 5.2 ɗin da ake tuhumar sa da sacewa.
Tun a cikin watan Yuli 2021 ne ICPC ta gurfanar da shi kotu, inda ake tuhumar sa da laifuka 18 da suka ƙunshi satar naira biliyan 18.
ICPC ta ce ya saci kuɗin tun daga lokacin da ya ke Rajistara na NECO har zuwa lokacin da ya ke Shugaban JAMB.
Idan ba a manta ba, cikin watan Afrilu 2020, PREMIUM TIMES Hausa ta buga cewa ICPC ta ƙwace kadarorin biliyoyin nairori daga hannun Ojerinde, waɗanda suka haɗa da makarantu masu zaman kan su, gidajen mai, gidaje a jihohin Kwara da Oyo, waɗanda ya mallaka ta hannun ‘yan-kore a Ilorin, Ibadan da Ogbomoso.
Akwai kuma wasu a Ile Ife a Jihar Osun da kuma Abuja.
A ranar Talata Ojerinde ya nemi Kotu ta ɗage Shari’a zuwa kwana ɗaya, domin a ba shi damar ƙulla yarjejeniyar ‘plea bargain’.
Sai dai kuma an ci gaba da shari’ar a ranar Laraba, yayin da lauyan ICPC Ebenezer Shogunle ya sanar wa kotu cewa yarjejeniyar ba ta yiwu ba.
Daga nan ne Oyewole ya ci gaba da shaida wa kotu yadda shi da Ojerinde suka riƙa kafa kamfanoni da kuma sayen manyan kadarori na shi Ojerinde ɗin, a lokacin ya na Rajistaran NECO da kuma Shugaban JAMB, shi kuma Oyewole ya na lauyan sa.
Ya ce baya ga kamfanoni takwas da manyan gidaje da gidajen mai, har tulin hannayen jari Ojerinde ya saya a bankuna.
Za a ci gaba da shari’ar a ranakun 4 da 5 Ga Afrilu, bayan an damƙa wa kotu kwafe-kwafen takardun shaidu na rasiɗai da satifiket na shaidun mallakar kadarori a lokacin gabatar da shaidar.
Discussion about this post