A ranar Juma’a ce Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da Sakataren Gwamnatin Tarayya cewa duk ministoci da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya ta tsarma ƙwararrun matasa a cikin dukkan Mambobin Hukumomi da Kwamitocin Gwamnatin Tarayya.
Umarnin ya zo bayan shekara bakwai da hawa mulkin Buhari, daidai lokacin da bai fi saura shekara ɗaya tal wa’adin mulkin sa ya cika.
Buhari ya bada umarnin a lokacin da ya karɓi baƙuncin ziyarar da Shugabannin Matasan APC suka kai masa.
Ya ce jefa matasa a cikin hukumomin zai taimaka masu sanin makamar aiki kuma zai kasance kamar wata cibiya ce a wurin su ta koyon ayyukan gwamnati da goyayyar siyasa.
Shugaba Buhari ya umarci Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ba shi rahoton yawan matasan da za a ɗauka a cikin kwamitocin hukumomin da har yanzu ba a kai ga kafawa ba, nan da watan gobe.
Daga nan kuma ya umarci Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari da ya tabbatar duk wata ana taron ganawa da ƙungiyar matasan na APC Youth Lobby group, domin a riƙa ganawar saurare da karɓar shawarwari.
Ya kuma yi kira ga dukkan manyan jami’an gwamnati su yi amfani da damar kafa kwamitin matasa da za su riƙa bibiya kuma su na sa-ido wajen ganin irin ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ke yi a dukkan faɗin ƙasar nan.
Ya ce kwamitin zai riƙa bayar da bayanan hali da yanayin ayyukan ke ciki domin ɗaukar rekod ɗin dukkan ayyukan ma manyan jami’an gwamnati ke yi ko suka ƙi yi ko suka ƙi ƙarasawa.
Sannan kuma Buhari ya amince a kafa Ofishin Tuntuɓar da Hulɗa da Matasa Na Shugaban Ƙasa. Sannan ya ce Sakataren Gwamnatin Tarayya da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa su gaggauta tabbatar da fara aikin ofishin.
Buhari ya shaida wa matasan, waɗanda su ka kai ziyara a ƙarƙashin jagorancin Ismaeel Ahmed cewa jam’iyyar APC za ta tabbatar cewa matasa sun riƙa samun guraben muƙamai a dukkan gwamnatocin tarayya, jiha da ƙananan hukumomi.
Discussion about this post