An bayyana cewa samar wa masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i da masana’antu yin tasarifin kuɗaɗe ta bankuna, hanya ce da za ta ƙara bunƙasa tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani.
Daraktan FSI Aituaz Kola-Oladejo ce ta bayyana haka, kuma ta ƙara da cewa bijiro da dabarun za su magance matsalolin da zamantakewar rayuwar jama’a da na tattalin arzikin su.
Yayin da ta ke cewa waɗannan matsaloli biyu tare su ke tafiya kamar tagwaye, ta yi bayanin ne cewa za a ƙaddamar da shirin cin moriyar wannan fasaha ce a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Minna (FUTMINNA).
Za a rungumi masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i su rungumi harkokin banki da inshora. Daga ranar 9 zuwa 11 Ga Maris za a fara a FUTMINNA.
An kuma fara yin rajista tun a ranar 28 Ga Janairu. Kuma za a ƙare a ranar Laraba, 16 Ga Fabrairu da ƙarfe 11:59 na dare.
A Shiga Nan: https://bit.ly/Include_Me
“Mun amince tare da yanke shawara cewa za mu haɗa guiwa da Jami’ar FUTMINNA domin samo mafitar waɗannan ƙalubale, duk da cewa su ɗaliban na fuskantar irin ƙalubale a kowace rana.” Inji Kola-Oladepo.
Sanarwar ta ce sana’o’i da dama a Arewacin Najeriya ba su rungumar tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta bankuna a kowace rana. Kuma su na kama kuɗaɗen a kullum.
“Saboda ko dai wasu sana’o’in sun yi masu tsaurin yin su ta tsarin tasarifin hada-hadar kuɗaɗe ta bankuna da kuma sadarwar zamani, ko kuma su na samun babbar matsalar kasa samun damar yin amfani da tsarin a sauƙaƙe.
“To amma yanzu idan aka buɗe shirin ko tsarin, zai samar da ayyukan yi da kuma dama ga ƙananan sana’o’i ya hanyar hikimar ƙwarewa da harkokin fasaha a Najeriya.
“Kuma wannan ƙalubale ne ga kowane ɗan Najeriya da ke karatu a jami’a.”
FSI ta ce binciken su ya nuna akwai ƙananan masana’antu a Arewa fiye da miliyan 15.
Idan ba a manta ba, cikin Oktoba 2021 ne FSI samar da mafita daga kaka-gidan da tsarin hada-hadar kuɗaɗe da aka gada tun iyaye da kakanni a yankunan faɗin Najeriya, ciki har da wasu jami’o’i.
Discussion about this post