Maimartaba sarkin Daura Umar Faruk-Umar ya bayyana cewa kishin kasar Daura ce da ministan Sufuri Rotimi Amaechi ke da shi ya sa masarautar ta karrama shi da sarautar Ɗan Qmanr Daura.
Sarki Umar-Faruk ya ce saboda lishin kasar Daura ya sa minista Amaechi ya kawo jami’ar Sufuri aka kafata a Daura sannan kuma da titin jirgin kasa da za a yi daga Najeriya zuwa ƙasar Nijar wanda zata ratsa ta Daura.
” Idan aka kyakkyawar nazari za a ga cewa tabbas mutanen Daura za su amfana da waɗannan abubuwa musamman titin jirgi.
” Za a samu tasha a Daura wanda hakan zai bunkasa kasuwanci a tsakanin mutanen mu a ciki da wajen Najeriya.
” Mu a masarautar Daura muna karrama duk wanda ya cancanta ne ba don kuɗi muke yin abubuwan mu ba. Dalilin haka ya sa har baki da ga wasu yankunan kasar nan da wajen Najeriya ma mukan karrama su da sarautu domin nuna godiyar mu kan soyayyar da suka nuna mana.
” Ba dalilin kuɗi ko wani abu bane ya sa muka karrama Anaechi da sarautar Ɗan Amanar Daura, masu cewa wai an bamu kuɗi ne ya sa muka yi wannan naɗi, sun shirga karya. Ba haka bane.
Bayan Amaechi, masarautar ta naɗa Nasir Haladu Danu sarautar Tafida Babban Daura.
Gwamnan Katsina Aminu Masari, Ministan Wasanni, Sunday Dare, Adamu Adamu na Ilimi, Olorunnimbe Mamora na Kiwon Lafiya, da Festus Keyamo na daga cikin waɗanda suka halarci naɗin sarautar a garin Daura.
Discussion about this post