Ya kamata a kyautata wa Osinbajo zato cewa bai taɓa fitowa ya nuna buƙatar tsayawa takarar shugabancin Najeriya, domin ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023 ba.
Sai dai kuma ko makaho ya shafa hoton Osinbajo, zai iya rantsewa ya na son kujerar. Ba don komai ba, sai saboda shi ne na biyu ga Shugaba Buhari, kuma ya fi kowa kusanci da kujerar, baya ga mai ita a yanzu, wato Buhari ɗin.
Ba ɓoyayyen abu ba ne ga kowa a ƙasar cewa Osinbajo yaron Tinubu ne. Kuma Tinubu ɗin ne ya amince ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa, amma ba don ya so ba, saboda kawai an ƙi amincewa Tinubu ya zama Mataimakin Buhari a zaɓen 2015.
Sannan kowa ya san Tinubu ya fi Osinbajo maita da kwaɗayin son zama shugaban ƙasa.
Haka kuma ƙungiyoyi daban-daban sun fito su na kaɗa gangunan neman Osinbajo ya fito takara, su na kashe maƙudan kuɗaɗen kamfen, zirga-zirga da tuntuɓa. Babu wanda ya san mai ɗaukar nauyin su, domin dai hatsi a gona ba ya kai kan sa cikin gari, sai wani ya ɗauka ya kai shi.
Har yau Osinbajo bai nesanta kan sa daga masu neman ya fito ba, kuma bai taka masu burki ba. Su kuma sai ƙara ƙarfi su ke yi, daga sama har ƙasa.
Bayanan ƙadda-ƙanzon-kuregen da ake yaɗawa a cikin ƙasar nan na nuna cewa an fi son Osinbajo ya fito fiye da TInubu. Shi kuma Tinubu har yau saboda yakana kuma ya na kan mulki, bai kai ga bayyana ra’ayin sa ba tukunna.
Duk da cewa sai cikin watan Yuni ake sa ran APC za ta yi zaɓen fidda-gwani, kuma sai cikin Agusta za a rufe ƙofar karɓar ɗan takara, wasu abubuwa da su ka faru, musamman iƙirarin da Babban Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Siyasa, Babafemi Ojudu ya yi, inda ya nuna bijire wa tsohon ubangidan sa Tinubu, ya koma bayan Osinbajo a 2023, hakan ya nuna cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ya shirya wani abu a ɓoye. Kuma da ƙarfin sa zai fito idan ya tashi fitowa, tamkar fitar harsashen bindiga.
Me Osinbajo Ya Taka Ne Har Yaron Sa Ojudu Ya Yagalgala Rigar Tinubu?
Na Fi Ƙarfin Wasu ‘Yan Iska Su Rirsasa Ni Bin Tinubu A Zaɓen 2023 -Ojudu, Mashawarcin Buhari:
Yayin da aka fara kaɗa gangar zaɓen 2023, kuma har wasu jiga-jigai sun fara karkarwa su na kirari, ɗaya daga cikin wanda ya nuna maitar neman tsayawa takara a ƙarƙashin APC, shi ne jagoran jam’iyyar Bola Tinubu.
To sai dai tun tafiya ba ta ma kai ga batun fitowa yankan tikitin takara ba, Tinubu ya fara haɗuwa da cikas.
Wasu da aka riƙa danganta su da Tinubu sun riƙa fitowa su na ƙaryatawa, musamman Ƙungiyar Yarabawa Zalla (OPC), Dele Mamudu da wasu daban.
Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a kan Al’amurran Siyasa, Babafemi Ojudu, ya fito ya bayyana cewa ba zai goyi bayan kamfen ɗin ubangidan sa Bola Tinubu ya zama shugaban ƙasa ba.
Ojudu wanda yaron Bola Tinubu ne a baya, ya ce amma fa kada jama’a su ka matsayar da ya ɗauka a matsayin cin amana.
Cikin Wata sanarwar da ya fitar a shafin sa na Facebook a ranar Talata, Ojudu wanda ya ce shi da Tinubu sun daɗe su na tafiya tare, “to amma a gaskiya mutunci na da tunanin da zuciya ta ke nuna min, ba daidai ba ne na goyi bayan Tinubu ya zama shugaban ƙasa.”
Ojudu da Tinubu sun fara shaƙuwar siyasa tun farkon 1990, inda tsohon gwamnan Lagos ɗin da kuma ɗan jarida Ojudu, wanda ya koma ɗan siyasa ya zama sanata.
Tinubu ya narka kuɗi a mujallar TheNews, wadda mallakin Ojudu da wasu abokan sa ce a lokacin.
Sai dai kuma a cikin 2016, Buhari ya naɗa Ojudu Mashawarcin Shuagab Ƙasa a Harkokin Siyasa, kuma ya umarce shi da ya yi aiki tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.
Duk da cewa Tinubu ne tsanin da aka taka aka ɗora Osinbajo kan kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa, tun tafiyar ba ta yi nisa ba su ka raba hanya, babu jituwa a tsakanin su.
Ana ganin dai a yanzu Ojudu ya ɗauki hanyar goyon bayan takarar Osinbajo, kuma ya fara tallar sa a zahiri da baɗini.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, tsohon sanatan ya ce har an fara yi masa barazana, kuma iyalin sa ma ana yi masu barazana, saboda kawai matsayar da ya ɗauka ta ƙin mara wa Tinubu baya.
“Kada ma wani ya yi tunanin cewa zai iya tirsasa ni yin abin ca mutunci na da zuciya ta ba su amince min na yi ba.” Inji Ojudu.
“Masu yawan kiran waya ta su na yi min barazanar banza da wofi da masu neman su kunyata iyali na, su daina haka nan.
“Na san Tinubu. Ina girmama shi. Da yawan waɗanda ke goyon bayan sa a yanzu, ba su ma san wane ne Tinubu ba. Da sun san wane ne Tinubu da ba su tsaya su na tayar da jijiyar wuya a kan sa, har su na neman ci min mutunci ko kai min hari ba.
“Lokacin da Tinubu ya ƙi goyon bayan takarar Obasanjo a 2003, ba a kira shi maci amanar jinsin Yarabawa ba ko maci amanar Afenifere.
“Ya zaɓi abin da ran sa ya biya masa a lokacin, kuma tarihi ya yi masa hukunci da alƙalanci. To ni ma ina so tarihi ya yi min hukunci da alƙalanci.
“Kuma lokacin da Tinubu ya goyi bayan Olu Falae maimakon jagoran mu Bola Ige, ai babu wanda ya kira shi Tinubu ɗin maci amana.
“Ku kuma ƙananan ‘yan iskan da ke ta aiko min da saƙonnin waya ku na yi min barazana, ni da iyali na, kuma ku na surfa min zagi don na ƙi goyon bayan Tinubu, ku sani hakan ba dimokraɗiyya ba ce.
“Na shafe shekarun tasowa ta a rayuwa ina yaƙi da danniya da masu danniya da masu mulkin soja. To har yanzu a shirye na ke, kuma ba zan saki abin da zuciya ta ta fi kwantawa da shi ba, ko da kuwa za a ɗauki rai na.”
Kusancin Osinbajo Da Kujerar 2023:
Ganin yadda wasu a yanzu ke gwasale Atiku da Tinubu, su na cewa tunda sun tsufa su haƙura da takara, hakan alamomi ne na share wa irin su Osinbajo hanya.
Musanman ma shi Osinbajo ɗin wanda ya fi kowa kusa da kujerar. Tsalle ɗaya kaɗai zai yi ya dira a kan ta.