Kamfanin Kula da Harkokin Fetur na Ƙasa (NNPC) ya fallasa sunayen kamfanonin dillalan fetur ɗin da suka shigo da gurɓataccen fetur a Najeriya, wanda ake taƙaddama a kan sa.
NNPC ya ce kamfanin harkokin shigo da fetur na Oando, A.Y Maikifi, Duke Oíl, Emadeb da Hyde ne suka shigo da shi, kuma daga Tashar Jiragen Ruwa ta Antwerp, ta ƙasar Belgium.
Shugaban NNPC Mele Kyari ya ce masu duba ingancin fetur sun yi sakacin ƙin duba ingancin fetur ɗin a lokacin da ake sauke lodin sa bakin ruwa.
An dai ƙiyasta cewa gurɓataccen fetur ɗin zai kai lita miliyan 100.
Sanarwar ta ce jami’an NMDRA sun binciki man, amma ba su yi binciken ko akwai man sinadarin Methanol a ciki ba.
Wannan sanarwar ta fito ne kwana ɗaya bayan Karamin Ministan Harkokin Fetur, Timipre Sylva ya shaida wa manema labarai cewa za a yi gagarimin bincike a gano waɗanda ke da hannu a cikin hada-hadar shigo da man.
A ranar Laraba PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa: Aikin Gama ya gama, an bar Gwamnatin Tarayya da bincike.
A cikin labarin, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta yi gagarimin binciken ƙwaƙwaf domin bankaɗo yadda aka shigo da gurɓataccen man fetur a cikin ƙasar nan.
Ƙaramin Ministan Harkokin Fetur Timipre Sylva ne ya bayyana wa manema labarai haka a Faɗar Shugaban Ƙasa, yau Laraba, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa tare da Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari dai shi ne Ministan Fetur, kuma a ƙarƙashin Ma’aikatar sa ce aka shigo da wannan gurɓataccen fetur ɗin, wanda za a yi bincike.
Haka kuma a ranar Laraba ɗin ce Hukumar Kula da Haƙo Fetur ta NMDPRA ta bayyana cewa fetur ɗin da ke ajiye a manyan tankunan Najeriya ya ragu daga yawan wanda zai wadaci ƙasa cikin kwanaki 30, zuwa adadin yawan kwanaki 20.
Raguwar ta faru ne saboda an killace gurɓataccen da aka hana sayarwa.
Sylva ya ce za a bayyana sunayen kamfanonin da suka shigo da gurɓataccen fetur ɗin, nan ba da daɗewa ba.
“Ba mu tattauna wannan batu ba a wurin Taron Majalisar Zartaswa. Amma idan kun tuna ai jiya na zo mun gana da Shugaban Ƙasa kan batun. Ba ni ne ya kamata ya bayyana maku sunayen kamfanonin da su ka shigo da gurɓataccen fetur ɗin ba. Amma dai mu na kan bankaɗo su.”
“Ba zan yi saurin cewa komai ba tukunna. Amma dai Gwamnatin Tarayya za ta duba lamarin waɗanda motocin su suka lalace bayan sun sha gurɓataccen fetur ɗin.
“Za a yi gagarimin bincike, kuma ba so na ke ku yi sauri ku yanke hukunci ba. Amma dai za a yi gagarimin bincike domin gano kamfanonin da ke da hannu a ciki, sannan mu dawo mu fallasa maku sunayen su ɗaya bayan ɗaya.