Kotun majistare dake Abeokuta ta yanke wa wasu matasa huɗu abokai daurin zama a gidan kaso bisa dalilin kama su da laifin kashe budurwar daya daga cikin su mai suna Sofiat Okeowo dake da shekaru 20 domin yin asirin kuɗancewa.
Alkalin kotun I. O Abudu da ya yi watsi da rokon sassaucin da matasan suka nema ya ce za su zauna a kurkukun har sai kotu ta kammala yin shawara da fannin da ake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka.
Kotu ta daure Balogun Mustakeem mai shekara 20, Abdulgafar Lukman mai shekara 19 da Waris Oladeinde mai shekara 18 wanda da shi aka hada Baki domin a kashe budurwarsa.
Kotun ta daure matasan bisa laifin hada baki da kisa.
Lauyan da ya shigar da karar Lawrence Balogun ya ce matasan sun aikata laifin ranar 28 ga Janairu a kauyen Kugba dake Abeokuta.
Balogun ya ce matasan bayan sun lallabi marigayiya Sofiat zuwa cikin gidan su sai suka datse kanta da adda.
Ya ce bisa ga bayanan da matasan suka bada sun ce sun kashe Sofiat ne domin su yi asirin kuɗancewa.
Balogun ya ce laifin da matasan suka aikata ya karya sashe 324,316 na dokar hukunta masu aikata laifuka irin haka na jihar Ogun na shekara ta 2006.
Iyaye basu sauke nauyin da aka ɗora a kansu na tarbiyartar da ‘ya’yansu su zama mutane na gari.
Discussion about this post