Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto ta gabatar da ‘tubabben’ likitan gogarma Bello Turji gaban ‘yan jarida.
An gabatar da Abubakar Hashimu ne a gaban ‘yan jarida, ranar Litinin.
Abubakar Hashimu shi ne ya riƙa yi wa Bello Turji da wasu ‘yan bindiga magani ya na kula da jinyar su shekaru uku da suka gabata, bayan su Turji sun sha kashi a hannun sojoji, har an harbe shi a kai.
Gogarma Bello Turji ya addabi yankunan Zamfara da Sokoto ya na fashi, samame da garkuwa da mutane.
Lokacin da ya kama mahaifin Kakakin Majalisar Jihar Zamfara, ya ƙi yarda ya karɓi kuɗin fansa, har dattijon ya mutu a hannun sa.
Ya riƙa ƙaƙaba wa mutanen yankin da ya mamaye haraji. Kuma a baya ya naɗa wa wasu ƙauyuka biyu na gabacin Sokoto dagatai.
Yayin da aka kama Abubakar Hashimu, ya yi wa ‘yan jarida ƙarin hasken asalin dangantakar sa da su Bello Turji.
Yadda Musa Karmanawa Ya Haɗa Ni Da Bello Turji, Har Na Zama Likitan Sa -‘Likitan’ Turji
Abubakar ya ce shi dai ya na da kemis ne a cikin Sokoto, kuma jami’in kiwon lafiya ne.
“Wata rana sai Musa Karmanawa ya zo ya same ni, ya ce na zo mu je na yi wa su Bello Turji maganin harbin da aka yi masu.
“Ya ɗauke ya kai ni wurin su a cikin daji, kamar shekaru uku da suka wuce. Na iske Turji an harbe shi a kai. Wasu da dama kuma da raunuka a jikin su. Duk na sa masu magani, na kula da su.
“Daga nan na riƙa zuwa ina kula da su. Kuma akwai masu zuwa har cikin gari wuri na su na sayen magunguna. Akwai wata allura da ake kira ‘Pentazocine’, har ita su ke saye a lokacin.
“To amma Ni tun a lokacin daga baya na tuba. Kuma na gudu na bar ƙauyen mu Karmanawa, don gudun kada a kashe ni ko a kama ni.” Inji Abubakar.
Haka kuma an gabatar da wani mai suna Samuel Chinedu, wanda ya ke sayar wa ‘yan bindiga ‘pentazocine’ a kan Naira 18,500 duk guda ɗaya.
Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, mai kula da Shiyyar Sokoto ne ya gabatar da su inda ya yi ƙarin bayanin cewa kwanan nan an kama ‘yan bindiga 54, an kashe 23 a wasu hare-hare da ‘yan sanda suka kai masu.
Ya ce an samu nasarar kama bigigogi 32 samfurin AK47, samfurin Tashi-gari-barde (RPG) guda biyu, harsasai 2600, shanu 150 da ƙananan wayoyi samfurin Techno guda 16.
An dai kama Abubakar Hashimu ne bayan an kama Musa Karmanawa cikin shekarar da ta gabata.
Musa Karmanawa ne ya shaida wa ‘yan sanda yadda ya haɗa Bello Turji da Abubakar Hashimu, har su ka riƙa zuwa jiyyar su Turji a cikin daji.
Discussion about this post