Daidai lokacin da kwanaki uku ne kaɗai suka rage wa APC wa’adin da dokar INEC ta gindaya mata ta gudanar da gangami na ƙasa, jam’iyya mai mulki ta sanar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ranar da za ta yi taron na ta na ƙasa.
Dokar Zaɓe Sashe na 85 (1) na Dokar Zaɓe ta 2010 ya shar’anta wa kowace jam’iyya lallai ta sanar wa INEC ɗin ranar da za ta yi taron gangami, kwanaki 21 kafin ranar.
Bayan jam’iyyar ta sha fama da ƙaƙudubar rikici, a ranar Alhamis ta sanar wa INEC ranar da za ta yi taron ta.
Wasiƙar wadda APC ta aika a ranar 2 Ga Fabrairu, cewa za ta yi ta Gangami Na Ƙasa a ranar 26 Ga Fabrairu, 2022.
“APC na sanar wa INEC cewa ta shirya gudanar da Gangami Na Ƙasa a ranar 26 Ga Fabrairu, 2022.
“Mu na so wannan wasiƙa ta kasance ta zama sanarwa ga INEC, kamar yadda Sashe na 85 na Dokar Zaɓe ta 2010 ya tanadar.
“Muna so ku shirya turo mana jami’an INEC da za su zo wurin taron gangami domin su sa-ido su ga yadda taron da zaɓukan da za a gudanar za su kasance.” Haka dai wasiƙar wadda APC ta aika wa INEC ta ƙunsa.
Shugaban Riƙo kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mala Buni ne shi da Sakataren APC na Ƙasa, John Akpanudoedehe su ka sa wa wasiƙar hannu.
APC ta aika da wasiƙar duk kuwa da cewa wasu manyan jam’iyyar sun nemi a ɗaga ranar yin gangamin saboda har yanzu akwai waɗansu rigingimun da ba a kai ga warware su ba.
Reshen Mata na APC ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a ɗage taron gangamin har sai yadda hali ya yi.
Sun ce “yin taron gangami a wannan lokacin tamkar yin gini ne a kan tsandaurin ƙasar da ba shi da ƙwari.”
“Ran Shugaban Ƙasa ya daɗe, muna sanar da kai akwai jihohi har 14 da shugabancin APC ya rabu gida biyu, wato ɓangaranci.
“Sannan kuma har yau APC ba ta gama wartsakewa daga rikicin da ya haifar wa jam’iyyar asarar jihohin Ribas da Zamfara ba, a zaɓen 2019.
“Abin takaici, maimakon a warware irin waɗannan rikice-rikicen, hankulan gwamnonin APC da na shugabannin ta ya karkata kawai wajen ganin an yi taron da ba shiri ko kimtsi.”
Matan sun kuma yi kira a rushe Kwamitin Sasantawar da Sanata Adamu Abdullahi ke jagoranci.
Shi ma Mataimakin Bulalar Majalisar Dattawa, Sanata Uzor Kalu ya yi kira a ɗage taron, kada a gudanar da shi a cikin Fabrairu.
Discussion about this post