A shafin Facebook akwai shafuka da suka rada wa kansu suna BBC, kuma mutane na daukansu sahihan shafukan BBC ne. A yayin da ire-iren wadannan kungiyoyi ke amfani da kimar da BBC ke da shi a idon jama’a, an gano shafuka fiye da 30 a Facebook, wadanda ke kiran kan su shafukan labaran BBC.
A daya daga cikin irin shafuka mai suna BBC News Nigeria “ wato labaran BBC a Najeriya, an wallafa wani bidiyo mai tallar wata sana’ar da zata ninka jarin da mutun ya sa a sana’ar har sau biyu cikin sa’o’i biyu kacal da farawa, idan har mutun ya amince da shirin. Shafin na dauke da hoto mai tambarin BBC, sa’anan akwai bayanai dangane da labaran BBC a Najeriya.
Duk da cewa binciken Dubawa ya nuna wai duk wata sana’ar da ta kunshi ninka kudi zamba ce da kuma hanyar yaudarar jama’ar da ba su ji ba su gani ba, wasu masu amfani da shafin sun dauka gaskiya ne har ma suna neman karin bayani kan yadda za su zuba jari da jimilar kudin da ake bukata.
Sai dai bayanan da suka danganci tarihin shafin na nuna cewa an kirkiro shi ne ranar 15 ga watan Janairun 2022, kuma tun wannan lokacin abubuwa biyu aka wallafa a shafin, da wannan tallan ninka kudin da kuma babban hoton shafin.
Haka nan kuma wata kungiyar ta daban ta radawa kanta suna „BBC News NI“ wannan ma ba mallakar BBC ba ne. Shi ma ya wallafa wani tallan amma dangane da irin tsubbun da zai taimaka wajen kubutar da jama’a daga kangin talauci. Shi ma shafin bai dade ba, a watan Yulin 2021 aka kirkiro kuma shi ma tuni ya sami ma’abota sama da 200.
Wasu daga cikin kungiyoyin kuma sukan sami mambobi da yawa su yi ta wallafa musu labarai marasa tushe da batutuwa masu haddasa husumiya. Kyakyawar misali ita ce wata kunigiya mai suna „BBC News + BBC.“ Wannan kungiyar na da mambobi sama da dubu 20. Shafin na wallafa bayanai iri-iri kama daga addini, zuwa tsiraici da siyasa.
A shekarar 2015 aka kirkiro shafin sa’anan aka sauya sunan shi zuwa „BBC News +BBC“ a shekarar 2019. Duk da cewa ana wallafa batutuwa da yawan gaske a shafin, babu wanda ke da alaka da ainihin shafin BBC da abokan huldarta.
Bukatar daukar mataki cikin gaggawa
Akwai shafuka akalla 30 a facebook da ke basaja suna aika sakonni da wallafa labarai kamar shafin BBC na gaske amma kuma shafuka ne da ake amfani da su don yaudarar mutane. Wasu daga cikin wadannan shafukan sun sauya sunayensu har sau biyar, kuma mutane marasa alaka da BBC ne ke kirkiro shafukan. Bacin haka duk abubuwan da su ke wallafawa a shafin ba su da dangantaka da BBC. Daga talla sai yada manufofin da suka zo daidai da akidunsu.
Abin da ya fi ban tsoro shi ne fiye da kashi 80 cikin 100 na irin wadannan shafukan an kirkiro su ne tsakanin shekarar 2020 da 2011, kuma yawan ma’abotan da suka samu, za’a iya dangantawa ne kadai da sunan BBCn da suke amfani da shi. Akalla mutane sama da dubu 30 suke amfani da wadannan shafukan, a yayin da daya daga cikinsu ya ke da mambobi dubu 103. Alal misali, shafi mai suna „BBC NEWS“ na da mambobi dubu 103 kuma suna wallafa batutuwa dangane da siyasa, tsiraici, barkwanci da addini wadanda dukkansu ba su da wata alaka da BBC.
Yaya sahihancin irin batutuwan da su ke wallafawa?
Yawancin batutuwan da suke wallafawa sun jibanci farfagandan siyasa, addini, barkwanci da labaran da ba’a riga an tantance gaskiyarsu ba. Alal misali, a shafin nan mai suna BBC NEWS an wallafa wani labari tare da bidiyo dangane da dauki ba dadin da aka yi a iyakan da ke taskanin kasashen Indiya da Pakistan. Duk da cewa labarin ya yi alkawarin wai za’a ga yadda komai ya gudana a cikin bidiyon. Hoto daya ne a bidiyon kuma maganar ba ta fita da kyau. Dan haka ba’a ga komai ba.
Haka nan kuma, wai shafin shi ma mai suna BBC News ya wallafa wani rahoto dangane da tarzomar wasu matasa a jihar Deltan Najeriya. Labarin ya kasance da hoton wasu matasa a fusace suna dauke da abubuwa iri-iri a matsayin makamai.
Sai dai a kashin gaskiya, babu wata tarzoma kamar haka. Hasali ma an dauko hoton ne daga wani labarin da ya bulla a shekarar 2013 lokacin da aka sami wata takaddama tsakanin mazauna garuruwan Offa da Erin-ille a jihar Kwara. Amma kuma mutane har sun yi tsokaci dangane da batun, sa’annan alkaluma sun nuna cewa mutane sama da dubu 12 sun yi ma’amala da wannan labarin.
Sahihan shafukan BBC da ke Facebook
Sahihan shafukan BBC na da wata alama mai launin ruwan bula, kuma duk halattattun shafukan BBC ba kungiyoyi bane masu alamar “like” kamar yadda za’a gani nan da nan a shafukan bogin da muka lisafta. Wasu daga cikin shafukan sun hada da BBC News, BBC Comedy, BBC Pidgin, BBC Hausa, BBC Igbo da sauransu.
Manufofin Facebook dangane da yin basaja a matsayin wani
Manufofin facebook sun hana da yin basaja kuma a watan Afrilun 2017 kamfanin ya kaddamar da yaki kan yada bayanai marasa gaskiya a dandalin shi.
Sai dai duk da haka ire-iren wadannan shafuka masu basaja suna cin Karen su ba babbaka ba tare da an sanya mu su wani takunkumi ba. Daya daga cikin dalilan shi ne Facebook bay a iya gane wadannan shafuka na bogi idan ba kai karan su aka yi ba. Wannan ne ma ya sa shafin ya sake bayyana yadda ya kamata a kai karan irin wadannan shafukan na bogi.
BBC na sane da irin wadannan shafuka?
Har zuwa lokacin da muka rubuta wannan labarin, BBC ba ta amsa sakon email din da muka tura mata dangane da wannan batu ba, kuma bam u ga wani rahoton da ya nuna mana cewa kamfanin na sane da basajan da wasu mutane ke yi mata ba. Bacin haka, muna da kwararan hujjojin cewa wadannan shafuka ba su da wata alaka da BBC suna amfani da damar da suka samu ne kawai su yaudari jama’a.