Al’ummar ƙasar Senegal sun kwana cikin farin ciki da shagulgulan annashuwa, bayan Zakunan Teranga sun kai wa Fir’aunonin Masar farmakin da su ka nutsar da su a ruwa, suka tafi da kofi zuwa Dakar, babban birnin Senegal a karon farko.
‘Yan wasan Senegal dai sun nuna ba wasan banza suka je yi ƙasar Kamaru mai masaukin baƙi ba. Saboda haka nasarar lashe kofin da su ka yi, ba abin mamaki ba ce, domin ko a Gasar AFCON 2019 ta baya-bayan ma sai ta suka dangana da wasan ƙarshe, inda Aljeriya ta lallasa su.
Kafin nan kuwa a 2002 ma Senegal ta je wasan ƙarshe, amma ba ta lashe kofi ba.
Fir’aunonin Masar kuwa sun so su lashe kofin, domin huce haushin lallasa su da aka yi a wasan ƙarshe na AFCON 2017, da kuma abin kunyar da suka tafka a 2019, inda aka fitar da su a farkon zagaye na farkon gasar, wadda Masar ɗin da kan ta ta shirya.
Wasan ƙarshe dai bai yi wa Masar daɗi ba, ganin yadda korar da alƙalin wasan Masar da Kamaru a kusa da na ƙarshe, ya yi wa kociyan Masar ɗin, Carlos Quiroz. Hakan ya sa bai shiga filin ƙwallo domin wasan ƙarshe ba.
Yadda Sadio Mane Ya Kashe Babban Abokin Sa Salah:
Wasan ƙarshe wanda Senegal ta doke Masar da cin bugun fenatiri 4:2, Sadio Mane ne ya buga ƙwallon ƙarshe wadda ta bai wa Senegal nasara.
Mohammed Salah ya yi niyyar buga wa Masar fenariti na ƙarshe, sai dai kuma tun kafin a zo kan sa, aka yi nasara a kan su. Sai dai aka bar shi ya na kuka.
Salah da Mane sun kasance tamkar Messi da Ronaldon Afrika. Sai dai su kuma ƙungiya ɗaya su ke wasa, wato Liverpool, inda ko a can ɗin, babu kamar su.
Tarihin ƙwallon ƙafa a Ingila ba zai taɓa mantawa da su ba. Sun yi ƙoƙari sun ciwo wa Liverpool Kofin Champions League’, kuma a karon farko sun ciwo wa kulob ɗin Kofin Firimiya na Ingila, kofin da shekaru 30 Liverpool ne ƙoƙari amma ta kasa lashewa.
Mane da Salah Allah ya ba su farin jini a Turai, musamman a Ingila inda suke wasa. Hakan kuwa ya faru saboda abu biyu: Na farko ƙwarewa da gwanittar su a fagen wasa. Sai kuma yadda su ke nuna tsantsar tawakkali da Allah (SWT) a harkar wasan su. Waɗannan dalilai sun ƙara masu ɗarsashi a zukatan magoya baya da masu kallo baki ɗaya.
Kwarewar Salah da ba ta hana su nuna wa duniya cewa lamarin yin Allah ne, ba yin su ba ne. Shi ya sa a duk lokacin da suka shiga fili, sai sun yi addu’a kafin su fara buga ƙwallo. Haka nan idan suka jefa ƙwallo, sai sun yi sujadar godiya ga Allah.
Su biyun su na jan zugar ‘yan kallo a birnin Liverpool, duk ranar Juma’a idan sun je Sallar Juma’a.
Sai dai kuma a ranar Asabar, su biyun sun kafsa, inda Mane ya yi rinjaye kan Salah ta kowane fanni. Mane ya fi Salah yawan taɓa ƙwallo, kuma ya fi shi kai hare-hare. Sannan kuma ya fi shi taimaka wa ‘yan gaban sa domin su ci ƙwallo. ‘Yan bayan Masar sun kayar da Sadio Mane sau takwas, wanda hakan zai tabbatar da cewa ya zame masu ƙarfen ƙafa sosai. Sannan kuma duk da Mane ya ɓarar da bugun fenatiri ana cikin wasan, a ƙarshe dai kwallon da ya jefa ce ta yi sanadiyyar nutsar da Fir’aunonin Masar cikin ‘Bahar Maliya.’