1. Karas na dauke da sinadarin Vitamin A wanda ke inganta karfin Ido sannan da sinadarin lutein wanda ke kare Ido daga kamuwa da cututtuka kamar su yanar Ido, amosanin Ido da sauran su.
2. Karas na kare mutum daga kamuwa da daji
Akwai sinadarin ‘Carotenoids da Anthocyanins’ wanda ke samar wa jikin mutum kariya daga kamuwa da cutar daji kowace iri.
3. Kare mutum daga kamuwa da cututtukan dake kama zuciya
Akwai sinadarin ‘Potassium wanda ke kare mutum daga kamuwa da hawan jini sannan da sinadarin ‘Fiber’ wanda ke hana yawan kiba a jiki wanda ka iya hana bugawan zuciya yadda ya kamata.
4. Inganta garkuwan jiki
Karas na dauke da sinadarin Vitamin C da Iron wanda ke samar wa jiki kariya daga kamuwa da cututtuka.
5. Cin karas na taimakawa wajen kawar da murdewar ciki musamman idan mutum baya iya yin bahaya.
6. Kare mutum daga kamuwa da ciwon siga
Karas na dauke da sinadarin fiber, vitamin A, beta-carotene wanda ke hana mutum kamuwa da ciwon siga.
7. Kara karfin kasusuwan jikin mutum
Akwai sinadarin Vitamin K da Calcium wanda ke karfafa kasusuwa jiki.
8 – Karas na maganin hawan jini matuka
9 – Karas na gyara dasashi da hakora
10 – Karas na rage kiba
Discussion about this post