Tun ranar Alhamis da aka sanar da ni rasuwar Abdulaziz Dabo Lere, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, na fada cikin jimamin rasuwar wannan bawan Allah.
Da farko dai marigayi AbdulAziz mutum ne mai farin jinin jama’a wanda kowa ya shaide shi da son jama’a da zumunta sannan kuma ga saukin kai sa saukin mu’amula da mutane.
Ga shi dai matashi ne amma kuma ciwo ya kwantar dashi. Ya dade yana jinya da ko a halin jinyar marigayi AbdulAziz idan ya samu dan karfi da sarari ko yayane zai yi kokari ya gaggana da yan uwan da sauran abokan arziki ko da ko ta waya ce.
Gamuwa ta ta karshe da marigayi AbdulAziz a garin Kaduna gamuwa ce da ba zan taba matawa da ita ba.
Mun hadu da shi a farko shekarar 2020 a wani shagon saida kayan masarufi. Ko da na ganshi sai ya tsaida ni sannan mun dade muna hira. Daga ka ganshi ka san baya jin dadi amma haka ya tsaya ya dage muka yi ta hirar zumunta da abokantaka.
Sai da muka dauki kusan minti 30 muna hira, muna raha muna dariya.
Tun daga wannan rana ban sake ganin sa saboda yana yi na zirgazirga da hidimomin yau da kullum na rayuwa.
Duk bayan kwana daya ko biyu idan ka hadu da wani wanda yake da alaka da marigayi Abdulaziz ta hanyar abokantaka ko ‘yan uwantaka sai ya fadi maka wani abin yabawa game da marigayi AbdulAziz.
Wannan rasuwa ta sa yayi matukar jijjiga mutane da dama duk da fama da yayi yana jinya na tsawon lokaci.
Fata da addu’a na shine Allah ya yi wa abinda ya bari a baya albarka, ya gafarta masa kurakuran sa ya sa Aljannah ta zamo makomar sa, Amin.
Mu kuma da muke raye, Allah ya sa mu samu kyakkyawar shaida, ya sa mu cika da kyau da Imani. Marasa lafiya kuma Allah ya basu lafiya, Iyaye da kakannin mu Allah ya gafarta musu.
Allah ya jikan musulmai, Amin.
Discussion about this post