Sanata Rochas Okorocha mai wakiltar yankin Imo ta Yamma, ya ce ya na so ya yi takarar shugabancin Najeriya a 2023, domin ya zama shugaban da zai fitar da ‘yan Najeriya daga ƙuncin talauci, sannan kuma ya zarce Shugaba Muhammadu Buhari wajen yi wa ‘yan Najeriya aiki tuƙuru.
Okorocha ya ce tabbas Shugaba Buhari ya yi wa Najeriya da ‘yan Najeriya ayyuka masu yawa, to amma shi idan ya zama shugaban ƙasa, ayyukan da zai yi sai sun nunka na Buhari nesa ba kusa ba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya ke bayyana kan sa da gabatar da kan sa a matsayin cewa zai fito takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023.
Tun a cikin makon jiya ne Sanata Okorocha, wanda tsohon Gwamnan Jihar Imo ne, ya sanar wa ‘yan Majalisar Dattawa cewa zai fito takarar shugabancin ƙasa, a ƙarƙashin APC.
Sai dai kuma Hukumar EFCC ta maka shi kotu a ranar da ya ke ƙaddamar da kan sa a matsayin mai neman takara.
Okorocha ya ce Najeriya na buƙatar mutum irin sa wanda ba shi da ƙabilanci, wanda zai ƙara haɗin kan ƙasar nan tare da ɗinke ɓarakar ta, kuma wanda ya damu da halin da talakawa da sauran faƙirai ke ciki. Shugaba wanda zai iya samar da yalwar arziki ga ɗimbin ‘yan Najeriya. Okorocha ya ce duk waɗannan ai halayen sa ne.
Okorocha ya ce a daina cewa Buhari ba shi da gaskiya. Ya ce talauci ne matsalar Najeriya.
“A daina cewa ai ba mai gaskiya ba ne. A daina cewa Buhari ba ya ƙaunar Najeriya. Na sha faɗa a baya cewa matsalar ita ce talauci. Domin a ƙasar nan, idan matsalar naira biliyan 1 ta yi mana rumfa ta rufe mu, to abin da mu ke da muke da shi na magance matsalar bai wuce naira 10,0000 ba.
“Najeriya na bukatar mutum iri na a zaɓen 2023. Saboda zan shimfiɗa gwamnati mai ɗauke da wani sabon salo daban.
“Buhari na ƙaunar ƙasar nan, to amma ana kaɗa gangar ɓallewa da gangar yaƙi a wasu sassan ƙasar nan.”
Wannan jarida ta buga labarin yadda EFCC ta maka Okorocha kotu, daidai lokacin da ya ke ƙaddamar da takarar shugaban ƙasa a 2023
ASHAFA MURNAI
Hukumar EFCC ta maka tsohon Gwamnan Jihar Imo, kuma Sanata Rochas Okorocha a kotun Abuja, inda ake zargin shi da wani jigo a APC sun haɗe baki sun saci Naira biliyan 2.9
Ana tuhumar Okorocha ne tare wa wasu kamfanoni biyar, bayan wancan babban ɗan siyasa.
EFCC ta gurfanar da shi ne, bisa zargi 17 da ake yi masa, dukkanin su na satar kuɗaɗe.
PREMIUM TIMES ta mallaki kwafe-kwafen takardun da ke ɗauke da tuhumar da ake yi wa Rochas ɗin.
Sauran waɗanda ake tuhuma tare da Okorocha sun haɗa da Anyim Nyerere Chinenye, Naphtali International Limited, Prefect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited da kuma Legend World Concepts Limited.
An shigar da ƙarar a daidai lokacin da Okorocha ke ƙaddamar da buƙatar fitowar sa takardar zaɓon shugaban ƙasa na 23.