Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta tarwatsa gungun ƴan bindiga a kauyen Kurmin Kare dake karamar hukumar Chikun ranar Lahadi.
Ƙauyen Kurmin Kare na iyaka ne da babban titin Kaduna-Abuja da yayi ƙaurin suna wajen hareharen ƴan bindiga da yin garkuwa da matafiya.
Kakakin rundunar ASP Mohammed Jalige ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai ranar Litini a garin Kaduna.
Jalige ya ce rundunar ta tarwatsa ‘yan bindigan ne bayan rundunar ta samu bayanan siri game da wani mummunar bala’i da suke kokarin tafkawa a daidai suna zaman kitsa yadda za su aiwatar da wannan hari.
Ya ce nan da nan aka aika da jami’an tsaro suka yi musu diran bazata.
Jalige ya ce sun kashe ‘yan bindiga da dama sannan wasu sun gudu da raunin harsashi a jikin su.
“An kama bindiga kirar AK-47 da harsashi 10 a ciki, harsashin bindiga guda 180 da babban bindiga kira GPMG guda daya.
Ya ce jami’an tsaron sun fara farautan sauran ‘yan bindigan da suka gudu da rauni a jikinsu domin a hukunta su.
Jalige ya yi kira ga mutane da kai karar duk wani da suka gani da ranin harsashi a jikinsa zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
Discussion about this post