Akalla mutum 8 ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin dake kauyen Gidigori dake karamar hukumar Rafi a jihar Neja ranar Lahadi.
Mazauna kauyen sun ce ‘yan bindiga sun afka coci bayan an tashi ibadar safe da karfe 11 suka sace mutum 8 ciki har da fastan cocin.
Sakataren gwamnatin jihar Ahmad Matane ya tabbatar da aukuwar al’amarin ya na mai cewa gwamnati na tattara sunayen waɗanda ƴan bundigan suka sace.
Majiya a kauyen ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ƴan bindiga sun dira cikin cocin ne a lokacin da babban faston da mambobinsa, wato waɗanda aka sace suke ganawa bayan kammala ibada a wannan safiya bayan mutane sun watse sai suka ji an dira a kan su.
Majiyan ta ce kai tsaye ƴan bindigan suka afka cocin ba tare da sun biya ta ko ina a cikin gari ba.
Kauyen Gidigori na yankin karamar hukumar Rafi ne da ke da iyaka da Birnin-Gwari a jihar Kaduna da yankin jihar Zamfara.
Gwamnatin jihar Niger ta ce mutum sama da 151, 380 be suka rasa gidajen su a dalilin hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Discussion about this post