Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya yi raddi dangane da dakatar da shi daga sarautar Jakadan Bauchi da Majalisar Masarautar Bauchi ta yi.
An dakatar da shi ne a ranar Litinin, bayan masarautar ta zarge shi da hannu wajen rikicin da ya faru a Tafawa Ɓalewa da Ɓogoro, yankin da Dogara ya fito.
Rikicin wanda ya faru a ranakun 30 da 31 Ga Disamba, ya yi sanadiyyar kai wa tawagar Sarkin Bauchi da Sarkin Dass hari.
Sai dai yayin da ya ke maida raddi, Dogara ya ce lamarin dakatar da shi siyasa ce kawai wadda Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ke ta rura wutar ta.
A cikin wasiƙar dalilan dakatar da shi, an zargi Dogara da cewa ko jaje bai je ba kuma bai aika wa sarakunan biyu da aka kai wa farmaki ba.
A kan wannan, Dogara ya nuna cewa ya aika masu da jaje, kuma ya rubuta hujjar sa.
Dogara ya nuna cewa fitintinu ne kawai Gwamna Bala ke kutsawa a jihar, inda ya nuna cewa duk irin kama-karyar da Bala zai yi, to ya tuna da wata rana ba shi ne gwamna a Bauchi ba.
Sannan Dogara ya lissafo sunayen mutanen da Gwamna Bala ya riƙa dakatarwa, musamman masu riƙe da ssrautun gargajiya.
Yayin da Dogara ke ƙara zafafa raddin sa kan Bala Ƙauran Bauchi, tsohon Kakakin Majalisar Dattawa ya bayyana gwamnan da cewa duk wani ƙulle-ƙullen tsiya a Jihar Bauchi Bala ke kitsa su.
Daga nan ya rantse cewa ba shi da hannu a rikicin, kuma bai ma san an gayyaci sarakunan zuwa taron ba.
“Ko ma an gayyace su ɗin, ban san za su je ba, saboda a baya ma ba zuwa su ke ba.
“Ba ni aka fara dakatarwa a Bauchi ba. An dakatar da Wazirin Bauchi, an dakatar da Wakilin Birni, an dakatar da Sarkin Ningi duk kafin a dakatar da ni.
“A Bauchi Fir’auna ne ke yi mana yadda ya ga dama, kuma ina farin cikin cewa ni ne Musan Bauchi, wadda komai tsananin gallazawar da Fir’auna zai yi, a ƙarshe na kawo ƙarshen lamarin.”
Premium Times ta bada labarin cewa Masarautar Bauchi ta dakatar da sarautar Jagaban Bauchi kan Dogara.
Masarautar Bauchi ta dakatar da naɗin Jagaban Bauchi da ta yi wa tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara.
Cikin sanarwar da aka fitar a ranar Talata, an bayyana cewa dakatar da shi ɗin na da nasaba ne da rikicin da ya faru kwanan nan a Ƙananan Hukumomin Tafawa Ɓalewa da Ɓogoro, yankin da Dogara ya fito.
Galadiman Bauchi kuma Hakimin Zungur, Sa’idu Ibrahim ne ya yi sanarwar dakatar da rawanin Dogara, yayin da ya kira taron manema labarai a ranar Litinin a Bauchi.
Ya ce Majalisar Masarautar Bauchi ta dakatar da Dogara har sai bayan hukuncin da kotu ta yanke.
“Idan za ku iya tunawa, a ranar 4 Ga Janairu Majalisar Masarautar Bauchi ta bayyana matsayin ta dangane da rikicin da ya faru a Tafawa Ɓalewa da Ɓogoro a ranakun 30 da 31 Ga Disamba, 2021.”
Ya ci gaba da cewa “Masarautar Bauchi a lokacin ta yi Allah wadai da abin da ya faru, ta ce dabbanci ne kuma iskanci ne.
“Daga baya Majalisar Masarautar Bauchi ta sake nazarin rikicin, ta gano cewa akwai hannun wasu manyan yankin, musamman ganin ɗaya daga cikin su da a yanzu aka dakatar ɗin ko jaje bai je ba, kuma bai aika an je masa ba.”
Mutane da yawa na ganin dakatarwar siyasa ce kawai, domin tun bayan da Dogara ya koma APC ya fara samun rikici da Gwamna Bala Mohammed.