Hukumar EFCC ta ƙara gurfanar da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, inda aka sake ɗirka masa zarge-zarge guda 17 duk na laifin karkatar da kuɗaɗe a lokacin da ya ke Minista, zamanin mulkin Goodluck Jonathan.
Haka nan EFCC ta gurfanar da tsohuwar Ministar Harkokin Kuɗaɗe ta zamanin Jonathan, Nenadi Usman duk a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.
Ba su kaɗai aka maka kotun ba. Akwai tsohon Shugaban Ƙungiyar Shuagabannin Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa, Yusuf Ɗanjuma.
Sannan an haɗa da wani kamfani mai suna Jointrust Dimensions Nigeria Ltd.
Tun da barko dai EFCC ta caje su ne da aikata laifuka 17 wajen karkatar da Naira biliyan 4.6. Mai Shari’a Mohammed Aikawa ne alƙalin.
A wancan lokacin ba su amsa laifin su na sun wawura kuɗin ba, sai aka bayar da belin su.
An fara shari’ar ce a wancan lokacin, amma sai aka canja Aikawa daga Legos.
A ranar dai an karanta masu caje–caje amma duk ba su amsa cewa sun aikata ba.
A ƙarshen watan Nuwamba ne EFCC ta sake damƙe Femi Fani-Kayode a harabar kotu, bisa zargin sa da yin fojare na jabun takardun likita masu ɗauke da bayanan ƙarya cewa ba shi da lafiya.
Mai Shari’a ya ce a sake bayyana a gaban sa, a ranar 11 Ga Maris.
Premium Hukumar EFCC ta sake kama tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, bisa zargin sa da ake yi da laifin fojare ɗin buga takardun bogin da ya gabatar wa kotu, inda ya yi ƙaryar rashin lafiya, don ya kauce wa tuhumar zambar naira biliyan 4.9.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito a ranar Talata cewa an sake kama Femi Fani-Kayode a harabar Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, jim kaɗan bayan an ɗage shari’ar sa da ake yi zuwa ranar 24 Ga Fabrairu.
Rahotanni sun ce an zarce da Fani-Kayode kai-tsaye zuwa Ofishin EFCC da ke Legas.
Ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren bai yiwu ba, saboda an kasa samun lambobin sa kafin a buga wannan labari.
Kakakin Yaɗa Labaran Fani-Kayode, mai suna Florida Nzenwa cewa ba za ta iya cewa komai a kan lamarin ba tukunna, har sai ranar Laraba.
Ana tuhumar Fani-Kayode da bugawa da kuma mallakar takardun bayanan likita na jabu, domin ya kauce wa zuwa kotu amsa tuhumar da ake yi masa.
Tuhumar Da Ake Wa Fani-Kayode: Ana tuhumar sa da laifin zambar naira biliyan 4.9 tare da waɗansu mutum biyu, da su ka haɗa da tsohuwar Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Nenadi Usman, tsohon Shugaban Kungiyar Ciyamomin Ƙananan Hukumomin Najeriya (ALGON), Yusuf Ɗanjuma.
Ƙin halartar kotu da Fani-Kayode ya yi ya sa kotu ta ci tarar sa naira 200,000.
Zaman baya bayan nan da aka yi ne lauyan Fani-Kayode ya shaida wa kotu cewa wanda ya ke karewar ba zai samu damar zuwa kotu ba, saboda ya na kwance a babban asibitin Kubwa, ba shi da lafiya. Kuma ya gabatar ta takardun likita tun kafin wannan zaman.