Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP, Raymond Dokpesi ya fara roƙon al’ummar jihohin yankin Kudu-maso-gabas su mara wa Atiku Abubakar baya, domin ya cika burin sa na zama shugaban ƙasa.
Dokpesi wanda ɗaya ne a cikin mambobin iyayen PDP, ya yi wannan kiran ne lokacin da ya ke wa jiga-jigan PDP na jihar Abia jawabi a Umuahia a ranar Litinin.
Dokpesi ya bada tabbacin cewa idan aka zaɓi Atiku ya zama shugaban ƙasa, to zango ɗaya na shekaru huɗu kaɗai zai yi, daga nan zai miƙa takarar shugabancin ƙasa na PDP ga ɗan ƙabilar Igbo.
Ya ce ya yi amanna yankin Kudu maso Gabas ya cancanci mulkin ƙasar nan, kuma ƙarya ake yi masa da ake cewa wai ya ce ƙabilar Igbo ba su cancanci mulkin ƙasar nan ba.
Ya ƙara da cewa masu haƙilon ganin ɗan ƙabilar Igbo ya shugabanci ƙasar nan, su na da hujja abin dogaro, domin yankin ya daɗe a matsayin saniyar-ware. “Don haka ya na buƙatar a ba shi dama idan Atiku ya yi zango ɗaya.”
Ya ce akwai buƙatar a yi wa Arewa dattako a yanzu a bar Atiku ya ƙarasa wa’adin da Arewa ba ta kammala ba, tun bayan rasuwar marigayi ‘Yar’Adua, kafin a bai wa ɗan ƙabilar Igbo tukunna.
Discussion about this post