A farkon shekarar nan ce Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta tsara gudanar da zaɓuɓɓukan cike gurabe da su ka rage a mazaɓu shida a jihohi huɗu a ranar 26 ga Fabrairu, 2022.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilmantar da Masu Zaɓe na hukumar, Mista Festus Okoye, ya saki a yammacin ranar Juma’a a Abuja.
Okoye ya ce an yanke shawarar hakan ne a wajen taron mako-mako da INEC ke yi a ranar Alhamis da kuma wani taro na musamman da aka gudanar a ranar Juma’a inda aka tattauna kan al’amuran da su ka janyo samuwar guraben da za a cike da saka ranar zaɓuɓɓukan da kuma yanayin tsaro a wasu daga cikin jihohin da abin ya shafa.
Okoye ya ce an yanke shawarar ne bayan da kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya da kakakin Majalisun Dokoki na wasu daga cikin jihohin su ka bayyana samuwar guraben.
A cewar Okoye, guraben su ne Mazaɓar Tarayya ta Akure ta Arewa/ Akure ta Kudu; Mazaɓar Tarayya ta Jos ta Arewa/Bassa a Jihar Filato, da Mazaɓar Jiha ta Pankshin ta Kudu, ita ma a Filato.
Sauran su ne Mazaɓar Tarayya ta Ogoja/Yala a Jihar Kuros Riba, da Mazaɓar Jiha ta Akpabuyo a Kuros Riba, da Mazaɓar Jiha ta Ngor-Okpala a Jihar Imo.
Okoye ya ce za a gudanar da zaɓuɓɓukan cike guraben a ranar 26 ga Fabrairu da zaran an kammala zaɓuɓɓukan ƙananan hukumin da ke Gundumar Birnin Tarayya (FCT).
Ya ce: “Wannan zai ba hukumar damar gamawa da yawancin zaɓuɓɓukan cike guraben, ta maida hankali kan zaɓuɓɓukan gwamnonin jihohin Ekiti da Osun da kuma shirye-shiryen da ake yi yanzu na babban zaɓen shekarar 2023.”
Babban kwamishinan ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin guraben sun samu ne a dalilin rasuwar waɗanda ke riƙe da muƙaman su a da; da tarwatsa tsarin gudanar zaɓe da aka yi da kuma cike muradin tsarin mulki kamar yadda doka ta tanadar a tsarin gudanar da zaɓe.
Ya ce INEC ta yanke shawarar haɗe zaɓen Mazaɓar Jiha ta Ekiti ta Gabas 1 da na zaɓen gwamnan Jihar Ekiti, wanda za a yi a ranar 18 ga Yuni.
Okoye ya kuma ce hukumar ta na tuntuɓar hukumomin tsaro da sauran muhimman masu ruwa da tsaki dangane da gurbin da aka samu a Mazaɓar Jiha ta Shinkafi a Jihar Zamfara.
Ya ƙara da cewa kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna bai bayyana samuwar gurbi a Mazaɓar Jiha ta Giwa da ke jihar ba.
Okoye ya ce za a wallafa sanarwar yin waɗannan zaɓuɓɓukan a ranar 24 ga Janairu.
Ya ce, “Jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓuɓɓukan su na fidda gwani, tare da kammala matsaya kan rigingimun da ka iya tasowa daga zaɓuɓɓukan fidda gwanin, tsakanin ranar 26 ga Janairu zuwa ranar 5 ga Fabrairu.”
Ya ƙara da cewa ranar ƙarshe ta miƙa wa hukumar jerin sunayen ‘yan takarar da aka tsayar ita ce 9 ga Fabrairu da ƙarfe 6 na yamma kuma tilas a yi hakan ta hanyar gidan yanar hukumar.
“Jam’iyyun siyasa za su miƙa sunayen wakilan su na zaɓe waɗanda za su tsaya masu ga jami’in zaɓe na ƙaramar hukuma kafin ko a ranar 12 ga Fabrairu kuma tilas ne jam’iyyun siyasa su tsaida kamfen na neman zaɓe a ranar 24 ga Fabrairu.
“Za a tanadar da kalmomin sirri na shiga gidan yanar don karɓar fom ɗin zaɓe daga ranar 5 ga Fabrairu a hedikwatar hukumar,” inji shi.
Ya shawarci jam’iyyu da su bi dokokin INEC dangane da ranaku da kuma Dokar Zaɓe ta 2010 (wadda aka gyara) wajen aiwatar da zaɓen fidda gwani fisabilillahi.
Ya yi gargaɗin cewa duk jam’iyyar da ta kawo sunan ɗan takarar da bai cike ƙa’idojin da aka gindaya a tsarin mulki da kuma Dokar Zaɓe ba, za a kama shi da laifi sannan idan aka yanke masa hukunci zai fuskanci tarar da ta kai N500,000.
Okoye ya ce a wajen tarurrukan, INEC ta kuma sake nazarin shirye-shiryen da ta yi na zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin Abuja da za a yi a ranar 12 ga Fabrairu.
Ya ce hukumar ta na kammala dukkan shirye-shiryen yin zaɓen.
Ya yi kira ga jama’a da su ka nemi yin sabuwar rajista da masu neman sauyin wuri da kuma masu buƙatar musanyar katin zaɓe (PVC) da su hanzarta karɓar su kuma su guji guje-gujen karɓa a ƙurarren lokaci.
Katin Sababbin Masu Rajista
Ya ce an riga an buga katittika na sababbin masu rajista da masu buƙatar tiransifa da masu buƙatar musanya, illa iyaka su je su ƙarɓa a ofisoshin dukkan ƙananan hukumomin da ke cikin gundumar ta FCT.
Ya ce, “Hukumar za ta ci gaba da bayar da bayanai a kai a kai kan shirye-shiryen da ta ke yi wa waɗannan zaɓuɓɓukan a kwanaki da makwanni masu zuwa.”
Okoye ya ce a ƙoƙarin INEC na yin aiki tare da masu ruwa da tsaki a tarurrukan da ta ke yi a kai a kai, za ta zauna da jam’iyyun siyasa a ranar 18 ga Janairu.
Ya ce hukumar za ta kuma gana da ƙungiyoyi masu zaman kan su a ranar 19 ga Janairu; za a yi taron kwamitin tuntuɓar hukumomi kan tsaro a harkar zaɓe (wato ‘Inter-Agency Consultative Committee on Election Security’, ICCES) a ranar 20 ga Janairu, da kuma kafafen yaɗa labarai a ranar 21 ga Janairu.
Discussion about this post