• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

    Almajirai

    UNICEF ta saka Almajirai sama da 20,000 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa karfi a Katsina

    Majalisar Tarayya ta ce a soke ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa ɗaliban jami’o’i da na Kwalejojin Gwamnatin Tarayya

    KALUBALEN DA KE GABAN MAJALISAR WAKILAI TA ƘASA: Gaganiya da matsalar raɗaɗin tsadar rayuwa, matsalar tsaro da sauran su da ake fuskanta a kasa

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    RASHIN TSARO: Tinubu ya amince da sayo jiragen sama masu saukar ungulu 12 ga sojojin Najeriya – Lagbaja

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    Ƴan ta’adda sun gamu da fushin sojojin Najeriya, sojoji sun kashe 50 sun kama 60

    GRAINS MARKET AT KAFIN MADAKI DISTRICT IN GANJUWA

    Yari ya raba tallafin tirela 145 cike maƙil da buhunan masara 145 ga mabuƙata a Zamfara

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

Yunƙurin Raba Kan Ƴanƴan Ɗarikar Tijjaniyyah, Saboda Hasadar Da Suke Yiwa Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
January 6, 2022
in Ra'ayi
0
Yunƙurin Raba Kan Ƴanƴan Ɗarikar Tijjaniyyah, Saboda Hasadar Da Suke Yiwa Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Ya ku bayin Allah! Abu ne da kowa ya sani, kuma ya amince, kuma babu wata jayayya akai, cewa hadin kan Musulmi wajibi ne, kuma rabuwa sharri ne, azaba ne kuma bala’i ne. Allah da Manzonsa (SAW) sun umurci Musulmi da su hada kan su. Kuma suka tabbatar masu da cewa, hadin kan nan shine sharadin zaman lafiyar su da ci gaban su. Idan Musulmi sun hada kai, zasu rabauta duniya da lahira. Idan kuwa suka rarrabu, suka ki bin umurnin Allah da Manzonsa, to lallai, tun anan duniya zasu ga mummunan sakamakon aikin su, kafin su tafi lahira, su hadu da Allah mahaliccin su.

Ya ku bayin Allah, wannan hadin kai da Allah da Manzonsa (SAW) suka yi umurni, shine Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yake kokarin rusawa, da sunan yakar Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, sanadiyyar hasadar da yake nuna masa, kuma wadda taki-ci-taki-cinyewa!

Abu ne da yake a fili karara cewa, tun lokacin da aka nada Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniyyah a Najeriya, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai yi kasa a gwiwa ba wurin yakar sa, kamar yadda yake ta yakar sa a can baya, saboda Sarkin ya dage akan cewa, dole ne ayi gaskiya.

Wallahi ba yadda Gwamna Ganduje bai yi ba na ganin cewa ya hana ayi nadin, to amma da yake duk abun da Allah yayi, dan Adam ba ya iya hanawa, sai da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tabbatar da wannan mukami na Khalifanci ga Khalifah Muhammadu Sanusi II.

Bayan da Gwamna Ganduje ya kasa soke nadin Khalifancin, sai ya yanke shawarar cewa bari yabi wata hanyar da duk zai bi, domin dai ya kawowa Sarki Muhammadu Sanusi II matsala. Sanadiyyar haka, sai ya dauki Ibrahim Dahiru Bauchi da Isa Sanusi Bayero (Isa Pilot) domin suyi aiki tare da shi, na ganin ya cimma wannan bakin buri nasa.

Gwaman Ganduje da wadannan mutane, sun yi yunkuri a lokuta daban-daban domin gudanar da zaman Zikiri a masarautar Kano, wanda wai a nasu tunanin, zai zama taron da ba’a taba yin irin sa ba a tarihin masarautar, amma duk basu ci nasara ba. Sai wannan karon kuma basu gajiya ba, suka shirya wani taron na Zikiri, wanda zai kalubalanci taron da aka shirya na duniya a garin Lokoja, domin gudanar da Maulidi tare da yiwa kasa addu’o’in zaman lafiya da samun ci gaba da hadin kai mai dorewa.

Ganduje da mutanen nasa, suna ganin cewa, su a irin nasu fahimtar, idan suka kira wannan taro a Kano, kuma suka sanya shi rana daya da wanda za’a yi a garin Lokoja, to lallai tabbas taron na Lokoja zai hadu da cikas. Kuma idan hakan ya faru, to sun cimma burin su, kuma sun kunyata Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II a idon duniya.

Amma da yake Allah baya zalunci, kuma ya haramtawa kansa zalunci, kuma ya hane mu da yin zalunci, kuma ya tabbatar muna da cewa, tabbas zai ci gaba da kunyata dukkan wani mutum azzalumi a duk inda yake, sai aka wayi gari yunkurin nasu ya hadu da cikas, kuma ya hadu da matsala.

Hakan ya faru ne saboda dukkanin Shehunan darikar Tijjaniyyah na Kano da sauran wurare, sun nuna cewa su fa suna tare da Sarki Muhammadu Sanusi II, kuma sun nuna cewa darikar Tijjaniyyah ba wata haja bace ta sayarwa, bare wani dan siyasa ya saye su da kudi. Sun nuna dattako, kuma sun yanke shawarar kaucewa duk wani abu da ya shafi yunkurin Gwamna Ganduje na zagon kasa ga darikar Tijjaniyyah da Khalifah Muhammadu Sanusi II.

Dukkanin Shehunnai da Khalifofin darikar Tijjaniyyah a Najeriya, sun fahimci abun da yake faruwa na yunkurin raba kawunan su, da kuma tarwatsasu da Gwamna Ganduje yake kokarin yi.

Ya ku bayin Allah! Wallahi wannan matsayi na kafatanin Shehunnan darikar Tijjaniyyah, ya kara jawo masu daraja da matsayi a idon duniya. Domin anyi yunkurin yin amfani da kudi, da kuma karfin gwamnati, amma suka kafe, suka ki yarda, suka zabi su kasance tare da gaskiya, da kuma masu gaskiya.

Kai yanzu ma su Shehunnan darikar Tijjaniyyah, yanzu sun gano wani yunkuri, da wata makarkashiya, na kokarin samar da wata kishiya da zata kalubalanci jagorancin Darikar Tijjaniyyah na duniya baki daya. Shi yasa aka dauki nauyin zuwa kasar Algeria, a dauko Shehunnai can, domin jagorancin da yake a kasar Senegal a yanzu, an kasa sayen su da kudi. Don haka, tun da basu mika wuya ba, to bari a manta da su, ayi hulda da Shehunnan kasar Algeria.

Shi yasa Gwamna Ganduje ya dauki nauyin ziyarar Ibrahim Dahiru Bauchi zuwa kasar Aljeriya akan ya gayyato wani Shugaban Darikar Tijjaniyyah, da sauran Shehunnai da Malamai, domin suzo Kano, domin yin Zikiri a ranar Juma’ah, 7 ga watan Janairun 2022, wai duk domin a dakile wancan muhimmin Zikirin da taron yiwa kasa addu’a, da za’a yi a garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi, wato a rana makamanciyarta, wanda gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Adoza Bello, ya roka ayi, kuma ya shirya a garin na Lokaja, kuma taron da Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II ne zai jagorance shi.

Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyyah ta koli ta jihar Kano, kakashin jagorancin Sheikh Abdullahi Uwais Limanci, ta yanke shawarar cewa babu ruwanta da duk wani abu na shirin raba kan al’ummah da Gwamna Ganduje yake son yi.

Idan dai har al’ummar kasar nan zasu iya tunawa, a can baya, Gwamna Ganduje ya bayyana Shehunan Darikar Tijjaniyyah, a matsayin wadanda ba zasu iya tabuka komai ba, domin ceto sarautar Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammdu Sanusi II, a inda yace duk addu’ar da suke yi ba zata yi amfani ba, domin wai “SUN KAMA KAFAR WALA”!

To yanzu dai alhamdulillahi, domin duniya ta yabawa Shehunan Darikar Tijjaniyyah na Kano, da na Najeriya baki daya, saboda sun nuna wa Gwamna Ganduje cewa su ba za’a iya sayen su da kudi ba. Dukkanin su sun yanke shawarar halartar babban taron da za’a yi a garin Lokoja, tare da wakilai daga Kaulaha da kasar Maroko. Kuma alhamdulillahi, galibin mabiya Darikar Tijjaniyyah a Najeriya, sunyi mubaya’ah ga jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaba daya tilo da Kaulaha da Maroko suka amince da shi.

Kuma alhamdulillahi, yanzu dai ta tabbata cewa, Gwamna Ganduje ya gaza a wurin yakar Darikar Tijjaniyyah, kamar yadda kuma ya gaza a wurin yakar Majalisar Malamai ta jihar Kano, a lokacin da yayi yunkurin tsige Malam Ibrahim Khalil saboda tsananin rashin kunya.

Kamar yadda kuka sani, Gwamna Ganduje da ‘yan kanzagin nasa, sun gayyaci dukkanin Shugabannin Darikar Tijjaniyyah na kasar Senegal, domin su halarci taron na Kano, amma shugabannin sunce sam ba zasu zo ba, domin ba zasu taba bayar da goyon baya akan abun da duk zai raba kan jama’ar su ba.

Ganin cewa Ibrahim Dahiru Bauchi ya kasa shawo kansu, shine sai aka tayar da jirgi na musamman, tare da su Isa Pilot, domin a dauki Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya tafi Senegal, domin a lallashi shugabannin darikar su amince suzo. Amma duk lallashin da aka yi, sun ce sam ba zasu zo Zikirin na Kano ba. To shine, suka samu wasu samari, matasa, daga kasar Senegal din, suka zo da su, domin su halarci taron na Kano, da sunan wai wakilan shugabannin. Idan hakan ya kasance, to wai su a ganin su, basu kunyata ba!

A can baya idan kun tuna, Gwamna Ganduje yayi amfani da wasu bara-gurbi, marasa kishi, ya samu nasarar ruguza Masarautar Kano mai tarin albarka, mai dimbin tarihi, mai cike da kima da kwarjini, wanda a halin yanzu ya mayar da Masarautar wani dandali na shiririta, ta hanyar zalunci.

Da ikon Allah, muna nan muna ta addu’a da rokon Allah, da fatan Allah ya kawo wa Kanawa da jihar Kano adalin Gwamna, wanda zai dawowa da jihar Kano, da kuma Masarautar Kano da kwarjinin nan nasu da Allah ya basu, kuma da ikon Allah, ya gyara dukkanin barnar da Gwamna Ganduje yayiwa jihar!

Sannan ina mai tabbatar maku da cewa, Gwamna Ganduje da duk ‘yan kanzagin nasa, ba zasu taba cin nasara a dukkan wani mummunan tanadi, da wani yunkurin sharri nasu ba. Kuma zasu ci gaba da takaicin abin da ya shafi Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II; domin shi Sarki Muhammadu Sanusi II wallahi yin Allah ne, ba yin kansa bane. Kuma liyafah da karramawa da aka yi masa kwanan nan a kasar Ghana, shaida ce dake nuna matsayinsa da daukakar darajarsa.

Kuma a daya gefen, ya kamata Gwamna Ganduje ya san da cewa, ikonsa da mulkinsa ba zasu iya tsallakawa zuwa ko’ina a Najeriya a fadin Najeriya ba, idan ba Kano kawai ba. Amma ikon Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, wanda yake yiwa hassada, wallahi ya wuce nahiyar Afirka, ya shiga duniya ko’ina. Wannan kuwa daga Allah ne.

Daga karshe, muna sanar da jama’ah cewa, bayan taron Zikiri da yiwa kasa addu’a, da aka saba gabatarwa a Masarautar Kano tare da Shehunnan darikar Tijjaniyyah, wato wanda ake gabatarwa a watan Muharram sau daya a shekara, bamu san da wani taron Zikirin da wasu suka shirya domin raba kan jama’ah ba. Muna kira, da ku kauracewa duk wata sanarwar gayyatar Zikiri da ake yadawa, wai za’a yi a Kano. Duk wani taro da bai sami izinin Khalifofin Shehu ba, kada su halarce shi. Dukkanin Shehunnai ba zasu halarta ba. Taron Lokoja shine halattacen taro. Idan kana da iko can zaka je. Idan kuwa babu halin zuwa, to ana kira ga ‘yan uwa da su zauna a zawiyoyinsu suyi Zikiri.

Kuma mun samu tabbataccen labari cewa an dauki nauyin ‘yan jagaliya, da wasu ‘yan kungiyoyi, da zauna-gari-banza, za’a biya su makudan kudade, domin su halarci taron da aka shirya a Kano din domin raba kan jama’ah. Wai da nufin su nunawa duniya cewa, sun shirya taron Zikiri, kuma an amsa kira. Don haka jama’ah, ayi hankali!

Alhamdulillah, a yau din nan, kuma a yanzun nan, da karfe biyar daidai (5:00 pm) na yammacin ranar alhamis, 06/01/2022, da nike wannan rubutu, domin sanar da duniya hakikanin halin da ake ciki, domin kar su yarda a rude su karyar banza, Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, shi da tawagarsa, da sauran Khalifofi, da Shehunnai da mukadamai, kai da duk wani mai fada aji a cikin Darikar Tijjaniyyah, a Najeriya da kewaye, duk sun sauka, sun halara a garin Lokoja.

Kuma yanzu ana tsakiyar cigaba da shirye-shiryen gabatar da Maulidi da Zikiri da yiwa kasa addu’a da rokon Allah na musamman, a garin na Lokoja, jihar Kogi.

Sannan ya ku bayin Allah! Ya ku masoya Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, ku sani, wallahi lokaci yayi da ya kamata mu nuna kishin mu tsantsa akan Khalifah Muhammadu Sanusi II. Ku sani, duk wannan kiyayyar da ake nunawa Khalifah Muhammadu Sanusi II ba komai bane illa tsantsar hassada, kiyayya da gaba. Hakan kuma bai samu ba sai da hadin kan Gwamnati, da kuma wasu bara-gurbi. Don haka, ya kamata soyayyar mu ta zama a zahirance, a aikace, zuwa ga Khalifah, ba wai a hoto kawai, ko a baki ba. Ya zama dole, kuma tilas, mu nuna, ta kowane hali, cewa, muna tare da Mai Martaba Khalifah Muhammadu Sanusi II.

Ina addu’a da rokon Allah ya karawa Khalifah lafiya, imani da nisan kwana; kuma Allah yasa ya ga bayan dukkanin makiyansa, amin.

Wassalamu alaikum,

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa ta lambar waya kamar haka: 08038289761.

Tags: AbujaNewsPREMIUM TIMESSanusiSarkiTijjaniyyah
Previous Post

‘Rudu da hauragiyar ‘yan siyasa ne kawai wai zan koma APC, amma kuma fa bari muga yadda gaba zata kasance’ – Kwankwaso

Next Post

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan Chana uku, sun kashe masu gadin su biyu a jihar Neja

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
BIDIYON HARBO JIRGI: Shirgegen Karya Boko Haram su ke yi – In ji Rundunar Sojin saman Najeriya

'Yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan Chana uku, sun kashe masu gadin su biyu a jihar Neja

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru
  • TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa
  • FCT ABUJA: Wike ya kori shugabanni da daraktocin hukumomi 21
  • Kotu ta yi watsi da ƙarar PDP a Shari’ar gwamnan Kaduna, dalili kuwa shine wai ba ta shigar da ƙara da wuri ba
  • MASHAHURAN JAMI’O’IN DUNIYA: Jami’ar Bayero ta fita kunya, Covenant da UI ne kawai ke gaba da ita a Najeriya

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Labarai
  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.