Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke ‘yan bindigan da suka kashe ‘yan sanda biyu a karamar hukumar Taura.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka kashe ‘yan sanda biyu a kauyen Kwalam dake karamar hukumar Taura.
‘Yan bindiga sun kuma yi garkuwa da Ma’aru Abubakar sirikin babban dan kwangila Haruna Maifata.
A taron da ya yi da manema labarai a garin Dutse kwamishinan ‘yan sandan jihar Aliyu Tafida ya ce an kama wadannan mutane a maboyar ‘yan bindiga guda uku a dajin Maizuwo dake kauyukan Dan Gwanki da Yandamo a karamar hukumar Sule Tankarkar.
Ya ce rundunar ta kama wadannan mutane ne bayan samun bayanan siri kan inda mahara ke boye.
Tafida ya ce an kama mahara 14 inda a ciki akwai maza 10, mata 4, sannan an cafke wani da ake zargi mai yin garkuwa dfa mutane ne dan asalin jihar Kaduna da yara 6 da ya sace.
” Bindigogi uku kirar AK-47, harsasai 308, babban bindiga kirar GPMG, naira miliyan biyu, adda daya, wayar salula guda shida, batiran wayar salula tara, layin wayar salula 12 da mota kirar Toyota Hiace bus ne aka kama a hannun su.
Ya kuma ce jami’an tsaron sun kwato bindigogi biyu na ‘yan sandan da aka kashe a Kwalam.
“Jami’an tsaron sun kwato babur na shugaban kungiyar ‘yan bulala Abdul Sajo da aka kashe a karamar hukumar Kirikasamma ranar Talata.
Tafida ya kuma ce jami’an tsaron sun ceto Hadiza Chadi Mai shekara 20 da aka yi garkuwa da ita a kauyen Marmara a karamar hukumar Kirikasamma ranar 8 ga Janairu.
Ya ce za a kai ‘yan bindigan kotu idan aka kammala bincike.