Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban makarantar firamare dake kauyen Buni Yadi Babagana Kachalla da wasu mutane hudu ‘yan kauyen Madiya dake karamar hukumar Gujba.
Kakakin rundunar Dungus Abdulkarim ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai ranar Laraba.
Abdulkarim ya ce Abubakar Barma, Haruna Barma, Modu Bukar da Hajiya Gana su ne mutum hudu din da aka yi garkuwa da su.
Ya ce ‘yan bindigan sun sace wadannan mutane ne da safe ranar Talata da misalin karfe 8:20 sannan rundunar ta samu labarin abin da ya faru a dalilin rahoton haka da wani Mala Boyema ya kawo ofishinsu da karfe 10:37 na wannan rana.
Boyema ya ce ya fada hannun ‘yan bindiga a Madiya yayin da yake hanyar zuwa wurin aiki inda bayan wani lokaci suka sake shi.
Jihar Yobe na daya daga cikin jihohin yankin Arewa maso gabashin kasar nan dake fama da hare-haren Boko Haram.
Sai dai Kuma yanzu abin ya canja salo inda yanzu ‘yan bindiga ne ke sace-sacen mutane a jihar.
A dai yankin Arewa jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina da Neja na daga cikin jihohin dake yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga babu kakkautawa.
Discussion about this post