Wani mazaunin garin Sabon Birni dake karamar hukumar Igabi, Jihar Kaduna Musa Bello ya tabbatar wa manema labarai cewa mahara sun afka cikin garin Sabon Birni kuma sun kashe muta ne da dama.
Zuwa yanzu dai, mutum 7 ne kawai aka iya tantancewa sun mutu, sai daia kuma kwamishinan tsaron Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa akwai yiwuwar yawan mutanen da maharan suka kashe ya fi haka yawa.
Musa ya ce ‘yan bindigan sun dira kauyen ne inda suka yi kan mai uwa dawabi da bindigogi suna ta harbe-harbe.
A karshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta karo yawan ma’aikata garin domin samun saukin hare-haren da ke aukuwa a yankin.