Ranar Talata ce kotu ta tura Hauwa Sa’idu Mohammed, wadda aka fi sani da Jaruma, zuwa kurkukun Kuje.
Nwoko, wanda hamshaƙin attajiri ne kuma tsohon ɗan majalisar tarayya, ya nemi ‘yan sanda su kama Hauwa, wadda aka fi sani da Maikayanmata, kuma su gurfanar da ita a kotu, saboda a cewar sa ta ɓata masa suna shi da iyalin sa suna, ta yi masu sharri da ƙazadi kuma ta yaɗa kalaman ƙiyayya a kan su.
Asalin Rikicin: Rikici tsakanin su ya fara ne lokacin da Jaruma ta shiga soshiyal midiya a shafin ta, ta yi wa Nwodo raga-raga, bayan saboda tsoma sunan ta da ya yi a cikin wata takardar da ya fitar a soshiyal midiya, mai ɗauke da dalilan rabuwar sa da matar sa Laila Charani, ‘yar ƙasar Marocco.
A cikin bayanan da Ned Nwoko ya watsa cikin watan Disamba, ya ƙaryata cewa ya rabu da matar sa ne saboda ta na amfani da sinadaran kayan mata na mallakar miji da Jaruma ke sayarwa.
Ned Nwoko wanda cikakken lauya ne da ya shahara a ƙasashen waje, kuma mijin fitacciyar jarumai Nollywood, Regina Daniels, ya ce “na rabu da mata ta Lailai Charani ‘yar ƙasar saboda ta je hutu Landan ta dawo da tsarabar iskanci da baɗala.”
Kama Jaruma:
Ned Nwoko us nemi ‘yan sanda su kama Jaruma saboda ta na sayar wa jama’a kayan batsa na mallakar miji ko maza, ba tare da lasisi, rajista ko amincewar hukuma ba.
Sannan kuma ya na so a kama ta a gurfanar da Jaruma saboda ta yi tinƙahon cewa laƙanin kayan mata da ta ba matar sa ne ya yi sanadiyyar mutuwar auren Chirani da shi.
Wani lauyan Ned mai suna Bryan Ukargbu ne ya sa wa wasiƙar hannu a madadin sa, mai ɗauke da kwanan watan 20 Ga Janairu, kuma aka turo wa PREMIUM TIMES a ranar Litinin.
Daga nan ‘yan sanda su ka kama Jaruma, amma aka sake ta bayan ta sha tambayoyi.
Bayan an sake ta, ta sake shiga shafin ta na soshiyal midiya, inda ta yi iƙirarin cewa an yi amfani da ‘yan sanda an kama ta don a buɗe mata ido.
‘Yan sanda sun gurfanar da Jaruma kotu a ranar Talata, inda Mai Shari’a ya tura ta kurkuku kafin ranar Juma’a, 28 Ga Janairu, ranar da za a koma kotu har a yi maganar beli.
Discussion about this post