Yayin da makonni biyu da suka gabata Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa duk wanda ya ci kuɗin Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta sai ya amayar, kuma sai an ɗaure shi, abin da masu karatu su ka manta shi ne, tun cikin watan Yuni na 2021 ne wanda ake zargi da wawurar biliyoyin kuɗaɗe mafi yawa, ya koma APC, har Shugaba Muhammadu Buhari ya yi masa kyakkyawar tarba a cikin jam’iyya mai mulki.
Nwaoboshi, Sanatan Da Ya Fi kowa ‘Dulmiya Hannu’ A Gurungunɗumar Harƙallar Hukumar NDDC, Ya Samu Kyakkyawar Tarba Cikin APC Daga Shugaba Buhari:
Sanata Peter Owaoboshi, wanda aka fi zarga da tafka babbar gurungunɗumar harƙalla a Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), ya sauya sheƙa zuwa APC, inda ya samu kyakkyawar tarba daga Shugaba Muhammadu Buhari.
Cikin watan Yuli ne dai NDDC ta zargi Nwaoboshi da harƙallar kwangiloli na naira biliyan 3.6.
An zarge shi da laifin yin amfani da sunayen kamfanoni 11 ya samar wa kan sa kwangiloli a NDDC, alhali kuma shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da NNDC ɗin da kuma Harkokin Neja Delta.
Nwaoboshi ya koma jam’iyyar APC, inda yau Juma’a Shugaba Buhari ya yi masa murnar komawa jam’iyyar mutane masu kawo sauyin ci gaban al’umma, wato APC.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege ne ya yi masa iso ga Buhari.
An dai zargi sanata da harƙallar kwangilolin da har Kakakin Yaɗa Labarai na Hukumar NDDC, Charles Odili ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba a taɓa yin harƙallar da ta fara muni a NDDC ba, kamar ta Nwaoboshi.
Idan ba a manta ba, Ministan Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya fallasa cewa da haɗin bakin ‘yan majalisa ake harƙalla a Hukumar Neja Delta.
Ya buga misali da cewa akwai lokacin da aka karkatar da dala miliyan 70 ta daɗe ajiye a wani banki.
Owaoboshi dai ya ƙaryata zargin da ake yi masa. Kuma har yau duk da ɗaukar hankali da Kwamitin Binciken Harƙallar NDDC ya yi cikin 2020, a Majalisa, har yau ba a lama kowa ba, kuma ba a hukunta kowa na.
Wanda aka fi zargin ma ga shi ya koma APC mai mulki, daga jam’iyyar PDP.
Badaƙalar NDDC: Hadimin Buhari Ya Cee Bai San A Hannun Wa Rahoton Binciken Ya Ke Ba A Yanzu.
Babban Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari kan Ayyukan Bunƙasa Yankin Neja Delta, Ita Enang ya bayyana cewa haƙiƙanin gaskiya a halin yanzu ba zai iya yin shisshigi ya ce ga a hannun hukumar da sakamakon binciken badaƙalar watandar kuɗaɗen Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta ya ke ba.
Yayin da ya ke amsa tambayoyi masu zafi a Gidan Talabijin na Channels, a ranar Talata, Enag wanda tsohon Sanata ne daga Jihar Akwa Ibom ya ce, “abin da kawai zan iya cewa shi ne, kwamitin bincike ya gama aikin sa, kuma ya miƙa sakamakon bincike ga Shugaban Ƙasa, ta hannun Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami.”
Enag ya ce to daga nan ba zai iya cewa ga hannun ɓangaren hukumar da sakamakon binciken ya ke ba.
Idan ba a manta ba, cikin 2020 ne Premium Times Hausa ta riƙa bin-diddigin buga labarin badaƙalar watandar maƙudan biliyoyin nairori a Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta, binciken da aka riƙa yi kai-tsaye a Majalisar Dattawa.
Makonni biyu da su ka gabata ne Buhari ya ce duk wanda ya ci kuɗi sai ya biya, kuma sai an ɗaure shi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da kakkausan harshe cewa dukkan waɗanda su ka ci kuɗaɗen Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta (NDDC) sai sun amayar da su kuma za a hukunta su.
Buhari ya bayyana haka a Jihar Akwa Ibom, a lokacin da ya ke buɗe wani katafaren ginin ɗakin kwanan ɗalibai a Jami’ar Uyo.
“Bari na sanar da ku cewa duk waɗanda su ka ci kuɗin da aka ware domin inganta rayuwar al’ummar Neja Delta, sai sun amayar da kuɗaɗen. Kuma za a hukunta su.”
Haka Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa Femi Adesina ne ya bayyana haka a ranar Alhamis.
Tuni dai Buhari ya bada umarnin a gudanar da binciken ƙwaƙwaf a NDDC, bayan samun rahoton cewa an yi shagalin da kuɗaɗen hukumar ta NDDD.
PREMIUM TIMES Hausa ta taɓa buga labarin yadda aka riƙa watandar maƙudan biliyoyin kuɗaɗe a NDDC.
An kuma gano yadda aka fara wasu ayyuka, amma aka watsar. Wasu kuma an nemi inda aka ce an fara su, amma ba a samu ko da wuri ɗaya ba a samu inda aka yi su.
Idan ba a manta ba, Ministan Bunƙasa Yankin Neja Delta, Godswill Akpabio ya taɓa cewa masu wawurar kuɗaɗe a NDDC sun maida kuɗaɗen hukumar kamar wata na’urar cirar kuɗi ta ATM machine, inda kowa ke cirar kudade irin yadda ya ga dama.
Adesina ya ce Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta (NRC) ta gina gidan kwanan ɗaliban da Buhari ya bude a jami’ar.