Har yanzu samun dabarun bada tazarar haihuwa ga mata matsala ce babba ga mata musamman waɗanda ba su da aure saboda fargabar nuna musu wariya da tsangwama a asibiti idan suka je neman ire-iren waɗannan magunguna domin amfanin kansu.
A Najeriya samun dabarun bada tazarar haihuwa ga macen da bata da aure na da matukar wahala domin sau dayawa malaman asibiti da sukan ci karo da na yi musu tsiwar cewa kamata ya yi su yi aure ne kafin su fara amfani da dabarun bada tazarar haihuwa.
A wasu wuraren ma dole sai mace koda tana da aure sai ta kawo wani shaidar izini daga mijinta.
Hakan da jami’an asibiti ke yi na matukar cutar da mata da dama a kasar nan inda matan da basu yi aure ba sukan samu matsala da mahaifar su saboda sun je cire cikin da tun farko ba su so dauka ba sannan ga mace mai aure ta ci gaba da haihuwar sati da Lahadi.
A jihar Oyo Adesuwa ta bayyana yadda rashin samun dabarun bada tazarar haihuwa ya sa ba za ta iya haihuwa ba har abada.
Adesuwa ta ce wata rana ta je asibitin gwamnati domin ta samu dabarun bada tazarar haihuwa saboda ta gaji da amfani da koro roba, kwayoyin da take sha da lissafin ranakun da ya kamata ta sadu da namiji idan har bata son daukan ciki.
Ta ce da ta je asibiti sai wata malaman asibiti ta ce baza ta bata magani ba saboda bata da aure wai tace ta yi aure tukunna sai ta zo.
Adesuwa ta ce ta dauki ciki duk da cewa tana amfani da kwayoyin hana haihuwa saboda ta yi kuskure wajen amfani da maganin.
Ta ce da bata ga al’adanta na wata ba sai ta yi gwaji wanda ya tabbatar mata cewa ciki ya shiga.
Adesuwa sai ta nemi kawarta wanda ta gaya mata kwayan maganin da za ta sha domin cikin ya zube.
Ta ce ta sha kwayan maganin kuma ta yi zubar jini sai dai bayan wani lokaci ta fara yin fama da ciwon ciki.
Da ta je asibiti likitoci sun bayyan mata cewa kwayar maganin da ta sha bai zubar da cikin ba sannan mahaifanta ya fashe kuma dole a yi mata aiki a cire mahaifan saboda kada ta mutu.
Adesuwa ta yi korafin cewa tun farko da malaman asibiti da ta gani tun farko ta amince ta bata maganin da wannan matsala da ta faɗa ciki bai auku ba.
Al’adun gargajiya da addini
Bisa ga al’adun gargajiya mata da dama na da ra’ayin cewa haihuwa Allah ne ke bada haihuwa.
A ra’ayinsu bai kamata mutum ya dakatar da haihuwa ba haka kawai idan Allah ya kawo.
A wani bincike da aka gudanar an gano cewa a yankin Arewacin Najeriya wanda musulmai sun fi yawa a yankin an fi samun karancin matan dake amfani da dabarun bada tazarar haihuwa.
Sannan sai kiristoci mabiya ɗarikar katolika inda kashi daya bisa uku ne kadai ke amfani da dabarun bada tazarar haihuwa.
Daga nan kuma sai sauran kiristocin dake yankin Kudancin kasar nan dake zuwa dariku daban daban inda kashi 41.4% ke amfani da tazarar haihuwa.
Bisa ga wannan sakamakon bincike addini da al’adun gargajiya na da mahimmiyar rawar da za su taka wajen ganin an wayar da kan mata sanin mahimmancin amfani da dabarun bada tazarar haihuwa a kasar nan.
Bayan haka akwai kuma matsalar camfe camfe da aka yarda da su.
Wasu matan sun camfi cewa idan har mace ta yi amfani da dabarun bada tazarar haihuwa ita da haihuwa kuma har abada wasu kuwa suna da ganin cewa amfani da dabarun bada tazarar haihuwa na lalata surar mace.
Zuwa yanzu burin gwamnati shine ta Samar wa akalla mata Kashi 27% dabarun bada tazarar haihuwa a kasar nan.
Ma’aikatar lafiya
Shugaban fannin dabarun bada tazarar haihuwa na ma’aikatar kiwon lafiya Salma Ibrahim ta bayyana cewa rashin ramar wa mata dabarun bada tazarar haihuwa matsala ce dake ci wa gwamnati tuwa a kwarya.
Salma ta ce ya zama dole a yi wa tubkar hanci idan har gwamnati na son yin nasara akan burinta na gani akalla mata kashi 27% na amfani da dabarun bada tazarar haihuwa a Najeriya nan da shekaran 2030.
Ta ce a dalilin haka ma’aikatansu ke kokarin wayar da kan jami’an lafiya kan mahimmancin bai wa mata masu aure da marasa aure dabarun bada tazarar haihuwa.
Salma ta kuma ce ma’aikatar za ta hada hannu da malaman addini da sarakunan gargajiya domin wayar da kan mata sannan mahimmancin amfani da dabarun bada tazarar haihuwa.