Kotun majistare dake Abeokuta jihar Ogun ta yanke wa wani magidanci mai suna Abass Moshood hukuncin zama gidan kaso na tsawon watanni shida saboda lalata kofar ɗakin da yake haya a ciki da gangar.
Alkalin kotun I. O . Abudu ta ce ta yanke wa Moshood wannan hukunci ne ba tare da bashi beli ba saboda ya furta da bakinsa cewa ya aikata hakan ne da gangar.
Dan sandan da ya shigar da karar sifeto Lawrence Balogun ya bayyana cewa Moshood ya aikata haka ranar 15 ga watan Janairu da misalin karfe 9:50 na dare a gidan hayan da yake zama dake layin Iwa a Sabo Abeokuta.
Balogun ya ce a wannan ranar Moshood da dan mai gidan da yake zama sun kicime, saɓani ya shiga tsakinsu inda shi Moshood ya rika cewa zai yi wa ɗan mai gidan dukan tsiya.
“Jin haka sai dan mai gidan ya gudu ya boye cikin gidan su. Cikin fushi sai Moshood ya balla kofar shiga gidan domin lakadawa yaron duka.
Ya ce gidan na wata Mrs Morufat Ogunsola ne kuma ita da kanta ta kai kara a ofishin ‘yan sanda.
Sannan kofar da Moshood ya balla ya yai naira 20,000 a kasuwa.