Wasu da ake zargin mahara ne a yau Labara sunyi awun gaba da wasu Yan kasuwa akan hanyarsu ta zuwa Kano a Dajin Birnin Gwari dake Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a dai dai dajin Unguwar Yako wanda yayi ƙaurin suna wajen satar mutane a hanyar ta Kaduna zuwa Birnin Gwari, inji Wanda abin ya faru akan idonsa amma ya nemi a sakaye sunansa.
Muna tafiya ne cikin jerin gwanon motoci da rakiyar sojoji amma wadanda sukayi gaba su aka tare aka nausa dasu daji, muna kallo ana tafiya dasu, inji direban.
“Mun tsaya cak a ƙauyen Unguwar Yako, amma da mu ka yi gaba, mun wuce motoci huɗu na ‘yan kasuwa babu kowa a ciki, duk an kwashe su. Mun kuma hangi ‘yan bindiga sun tasa ƙeyar su zuwa cikin daji.
Muhammad Jalige, Kakakin Yan Sandar Jihar Kaduna bai dauki wayar da akayi masa domin jin ta bakin hukumomin Yan Sanda.
Discussion about this post