Jigon jam’iyyar APC Bola Tinubu ya ɓulla a Katsina, ya ce Najeriya za ta kawo ƙarshen dukkan matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan.
Tinubu ya je Katsina domin yin ta’aziyyar Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Rabe Nasir, wanda aka yi wa kisan kulla watanni biyu da suka gabata.
Ya ce Jihar Katsina ta faɗa cikin jarabawa, amma ba da daɗewa ba Najeriya za ta kawo karshen waɗanda ƙalubale da ke damun sassan ƙasar nan.
“Lallai Jihar Katsina ta gamu da jarabawa ta matsalolin tsaro. To mu dai duk abin da ya samu ɗaya daga cikin mu, abin ya shafe mu.
“Mu tashi mu riƙa sa-ido, kuma mu riƙa yi wa juna nasihar muhimmancin zaman lafiya da juna. Mu yi ƙoƙarin sauya tunanin masu ƙoƙarin maida ta’addanci da hare-hare abin samar wa gindin zama a cikin al’umma.
“Ina kira ga Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin Shugaba Muhammadu Buhari kuma Kwamandan Askarawan Najeriya, ya yi duk abin da zai iya yi domin ya kakkaɓe masu hana ƙasar nan zaman lafiya.
“Za mu ci gaba da taya jihar Katsina jimami. Kuma mu na yi wa Gwamnatin Jihar Katsina addu’a ita da al’ummar jihar baki ɗaya. Allah ya sa mu ga ƙarshen wannan kashe-kashe da garkuwa da ake yi da mutane, ba gaira ba dalili.” Inji Tinubu.
Da ya ke jawabi, Masari ya ce matsalar Katsina ta fara ne daga satar shanu, wadda gwamnan ya ce fashi ne da samame a cikin yankunan karkara.
Ya ce a baya ‘yan bindiga a cikin jama’a su ke, ba a cikin daji ba. Sai da su ka yi ƙarfi ne sosai su ka koma daji, su na kama mutane su na karɓar kuɗaɗen fansa.