Dandazon ‘yan bindigar da aka ce sun kai 500 sun kashe mutum 12 a ƙauyen Illela da ke cikin Ƙaramar Hukumar Safana a Jihar Katsina.
Hatsabibin ɗan bindigar nan Ɗanƙarami ne da kan sa ya jagoranci yaran sa suka kai harin, saboda zargin cewa mutanen Illela sun ɓoye wani tubabben ɗan bindiga mai suna Mani Turwa.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina ya tabbatar da kisan mutanen.
Wata majiya kuma ta shaida wa wakilin mu cewa ‘yan bindigar sun ƙone wani sashe na garin ƙurmus.
Mani Turwa ya tuba daga aikata fashi da garkuwa da mutane cikin watan Afrilu, 2021, kuma ya yi ƙoƙari ya lallashi wasu ‘yan bindigar duk su ka damƙa wa hukuma makaman su.
Kafin Turwa ya tuba dai ya na yin fashi da garkuwa ne a yankunan Safana, Batsari da wasu yankuna.
Tubar sa ta kawo zaman lafiya a wasu yankunan, har da garin Illela.
Ya riƙa hana ‘yan bindiga su ka hari, ko dai ta hanyar yin fito-na-fito da su, ko kuma a duk lokacin da aka sanar da shi cewa za a kai hari, to zai je wurin ‘yan bindiga ya ba su haƙuri. Nan da nan Musa Turwa ya zama wani abin yabo kuma kowa na sa masa albarka a yankunan.
Wannan farin jini na Turwa ya ɓata wa Ɗanƙarami rai matuƙa. Har dai a ƙarshe ya yi tunanin afka wa Illela da hari, tunda a can aka karɓe shi da zama.
Majiya ta ce an kai harin a ranar Juma’a, kuma ba a kashe iyalin Turwa ko ɗaya ba.
Wata mata mai suna Mariya Yusuf da ke gudun hijira a Katsina, ta shaida wa wakilin mu cewa kusan rabin garin an banka masa wuta, yayin da mutanen garin wasu sun gudu zuwa Dutsin-ma, wasu kuma Katsina.
Shi ma Lawal Yusuf ya ce da idon sa ya ƙirga gawarwaki 12. Sannan ya ce “maharan sun kai su 500, domin kowane babur mutum uku ne a kan sa.”