Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya riga kowa nuna maitar neman zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Bai ɓoye wa kowa ba, kuma tun farko da ƙarfin aljihun sa ya fito, domin ya makance wajen yin bindiga da maƙudan kuɗaɗe ga ‘yan wasan Hausa na Kannywood, ana shirya masa waƙe-waƙe da tallolin tallata shi.
Allah ya kaɗai ya san yawan miliyoyin kuɗaɗen da Yahaya Bello ya yi bindiga da su kan ‘yan fim. Ya riƙa ɗirka masu kuɗaɗen al’ummar jihar sa, su kuma su na ɗirka masa waƙoƙi.
Haka kuma Allah kaɗai ya san miliyoyin kuɗaɗen da ‘yan fim su ka karɓa a hannun sa. Wanda bai taɓa mallakar ko amalanke ba, ya mallaki mota albarkacin Yahaya Bello.
Da yawan su sun riƙa kai masa ziyara. Yadda ake zuwa ziyarar kaburburan wasu waliyyai a shekarun baya, haka ‘yan fim daga Kano da Kaduna su ka riƙa zaryar ziyarar Yahaya Bello, ‘waliyin su’, mai ba su kuɗi ba jikara.
‘Yan fim da yawa a Kano sun fi wasu miliyoyin ‘yan Jihar Kogi cin moriyar gwamnan su Yahaya Bello.
A cikin shekaru biyu Yahaya Bello ya ɗauki nauyin shirya taruka da dama, waɗanda a siyasance, duk dai share hanya ce ya ke yi, ko ake yi masa ta neman takarar shugabancin ƙasar nan a ƙarƙashin APC.
Idan ya karɓi baƙuncin ‘yan wannan ƙungiya, gobe kuma ‘yan waccan zai karɓi baƙunci. Wataƙila ‘yan gudubale ne kaɗai ba su je sun kwashi rabon su a hannun Yahaya Bello ba.
A-wanki-gara: Yadda Wani Fasto Ya Ce Ya Ga Yahaya Bello Kan Kujerar Shugaban Najeriya:
Makonni biyu bayan gagarimin taron mabiya Ɗariƙar Tijjaniya a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, manyan limaman coci-coci daban-daban har su 1,000 sun yi taron yi wa Yahaya Bello addu’ar nasarar zama shugaban Najeriya.
A wurin taron, babban limami Bishof Prince Madaki ya rantse da Ubangijin talikai cewa Ubangiji ya nuna masa Yahaya Bello zaune a kan kujerar mulkin Najeriya. Ya ce su a yanzu kawai sai dai su ce lokaci kawai su ke jira kafin a rantsar da shi.
Yahaya Bello: Gauɗe Ba Ka Matanki:
Sai dai kuma Yahaya Bello na da ƙalubale a gaban sa. Akwai matsalar rashin ƙarfi kamar sauran ‘yan takara irin su Tinubu da Osinbajo a APC. Sannan kuma ya na da gauɗantar da ba za a so mutum kamar mai shugabancin Najeriya ya riƙa irin garangauɗancin sa ba.
Cikin 2020 gwamnatin tarayya ta sha fama da shi, inda ya ce a jihar Kogi babu wanda ya taɓa kamuwa da korona, kuma ya hana jami’an NCDC shiga jihar domin su bayar da shawarwari. A ƙarshe ma ƙaryata cutar korona ya yi.
Irin yadda magoya bayan Yahaya Bello su ka riƙa tafka rashin mutuncin da har ya kai aka banka wa gidan wata shugabar PDP wuta, kuma ta ƙone ƙurmus yayin zaɓen tazarcen sa, hakan na nufin Bello ba irin shugabannin nan ba ne da za a bai wa amanar shugabancin ƙasa mai mutum miliyan 200.
Yahaya Bello har yau ya kasa biyan mafi ƙarancin albashi na naira 30,000.00.