Zargi: wani labarin da ka wallafa a shafin soshiyal midiya na zargin wai duk wadanda suka taba zama gwamna a jihar Oyo sun rasu da suka kai shekaru 71 na haihuwa.
Wani labarin da aka wallafa a shafukan soshiyal midiya ranar 14 ga watan Janairu ya yi zargin cewa tsoffin gwamnonin jihar Oyo guda biyar duk sun rasu ne a lokacin da suka kai shekaru 71 cif-cif da haihuwa.
Labarin ya dauki hankali sosai kuma an yi ta yada shi a WhatsApp tare da jerin sunayen tsoffin gwamnonin jihar Oyon wadanda su ka hada da Bola Ige, Kolapo Ishola, Lamide (Lam) Adesina, Abiola Ajimobi da Adbayo Alao-Akala da cewa sun mutu da suka kai shekaru 71.
Jerin sunayen na hade da wani gajeren tsokaci kamar haka, ” Me za ku ce dangane da wannan?“ yana zargin wata kila ba haka nan suke mutuwa ba, wai akwai wani abin da ya yi sanadiyyar mutuwar su a wannan yawan shekarun wanda ba kowa ne ya sani ba.
Wannan labarin ya yi ta daukar hankali a kafofin sadarwa da dama musamman Whatsapp shi ya sa muka ga ya dace mu tantnace gaskiyar wannan lamari.
Tantancewa
Cif Bola Ige wanda ya kasance gwamnan jihar Oyo daga shekarar 1979 zuwa 1983 ya rasu ne a sanadiyyar harbin bindiga wanda aka kashe shi shi a gidan sa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ranar 23 ga watar Disembar 2001. An haifi Bola Ige a garin Esa Oke, da ke jihar Osun ranar 13 ga watan Satumban 1930. Shekarunsa 71 a lokacin da ya rasu.
Bincike ya kuma nuna mana cewa Cif Kolapo Ishhola ya rasu a shekarar 2011 lokacin yana da shekaru 77 na haihuwa. Kolapo ya zama gwamnan jihar Oyo daga shekarar 1991 zuwa 1993.
Lamidi Adesina ya kasance gwamna daga 1999 zuwa 2003. Alhaji Lamidi Adesina ya rasu a shekarar 2012 lokacin yana da shekaru 73. Adesina ya cika ne a asibitin St. Nicholas da ke jihar Legas bayan da ya yi gajeruwar jinya, idan da bai rasu ba, da ya cika shekaru 74 da haihuwa a watan Janairun shekarar 2013.
Sanata Abiola Ajimobi kuma an haife shi ne ranar 16 ga watan Disemban 1949 a Oja-Oba. Kuma ya kasasnce gwamna daga 2011 zuwa 2019.
Ajimobi ya rasu ne ranar 24 ga watan Yunin 2020 a wani asibitin kudi da ke jihar Legas bayan da ya shafe makonni yana fama da sarkakiyar da ya fiskanta sakamakon kamuwa da cutar COVIID-19. Shekarunsa 70 a lokacin da ya cika.
Otunba Christopher Adebayo Alao-Akala ya kasance gwamna daga shekarar 2007 zuwa 2011. Alao-Akala ya rasu a gidan shi da ke Ogbomoso ranar laraba 12 ga watan Janairun 2022 lokacn yana da shekaru 71 na haihuwa. An haife shi ranar 3 ga watan Yuni, 1950 a garin Ogbomoso da ke karamar hukumar Arewacin Ogbomoso a jihar Oyo.
Daga wadannan bayanai da muka samu, mun gano cewa ba duka gwamnonin ne suke da shekaru 71 da suka rasu ba. Cif Bola Ige ya rasu yana da shekaru 71 bayan da aka harbe shi a watan Disemban 2001, Kolapo Ishola na da shekaru 77 lokacin da ya rasu a shekarar 2011 a yayinda Alhaji Lam Adesina kuma ya ke da shekaru 73 na haihuwa lokacin da ya rasu a shekarar 2012.
Haka nan kuma Abiola Ajimobi ya kasance da shekaru 70 da wata 6 lokacin da ya rasu a watan Yunin 2020, shi kuma Alao-Akala na da shekaru 71 lokacin da ya rasu ranar laraba 12 ga watan Janairun 2022.
A karshe
Zargin wai tsoffin gwamnonin jihar Oyo duk sun rasu da suka kai shekaru 71 na haihuwa ba daidai ba ne domin Bola Ige da Alao-Akala ne kawai suka rasu suna shekaru 71.
Discussion about this post