‘Yan bindiga sun sako mahaifiyar Dan majalisar dokokin jihar Kano dake wakiltan Gezawa, Isyaku Ali.
Ali Wanda a da shi ne kakakin majalisar amma a yanzu yake rike da kujerar shugaban masu rinjaye na majalisar ya sanar da haka wa jaridar ‘Solacebase Newspaper’.
Ya ce an sako mahaifiyarsa Hajiya Zainab ranar Talata da safe bayan sun biya naira miliyan 40 kudin fansa.
Ali ya ce ‘yan bindigan sun sako mahaifiyarsa a yankin jihar Jigawa ne amma yanzu sun kama hanyar zuwa dauko ta.
Idan ba a manta ba a ranar 12 ga Disemba 2021 ‘yan bindiga suka sace Hajiya Zainab mahaifiyar dan majalisa Ali.
Ɗan Ali, Sani Ali ya shaida cewa maharan sun dira gidansu wajen ƙarfe 1 na dare, suka kutsa gidan su na neman a nuna masu ɗakin da mahaifiyar ɗan majalisar take kwance.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Honorabul Ali ya shaida wa jaridar cewa maharan sun karya ƙofar ɗakin gyatumar, su ka kutsa da ƙarfin tsiya, su ka fito da ita.
Tuni mahara sun fara addabar yankunan Kano da kewayen jihar.
Ba kuma wannan ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai hari a Gezawa ba, duk kuwa da cewa garin ya kusa haɗewa da Kano.
Cikin 2021 ne aka shiga har garin aka yi garkuwa da wani attajiri.