Wasu gungun ‘yan iska sun yi wa Oba Ayinde Odetola, Sarkin Agodo kisan-gilla, sannan suka banka masa wuta ya ƙone ƙurmus.
Agodo gari ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ewekoro ta Jihar Ogun.
An kashe basaraken tare da wani hadimin sa. Kuma dama wannan ne kisa na biyu bayan watanni uku baya an kashe wani daga cikin dangin basaraken.
Da rana wajen 11 na ranar Litinin ɗin nan aka kashe Sarkin, kamar yadda wata majiya daga garin ta shaida wa PREMIUM TIMES.
An kashe shi ne wajen rikicin neman wanda zai yi sarautar Olu na Agodo, tsakanin Gidan Sarautar Ake da Gidan Sarautar Owu da ke garin.
Wata ƙanuwar mamacin mai suna Adenike Akintade, ta bayyana cewa irin kisan da aka yi wa basaraken, irin sa aka yi wa ƙanen su a watannin baya.
“Yau da safen nan aka sallame ni daga asibiti. Ko hutawa ban yi ba aka kashe ɗan’uwa na. Na shiga jimamin rashin sa.”
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce basaraken ne kaɗai aka kashe.
Ya ƙara da cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ogun Lanre Bankole ya je garin, har wurin da aka yi kisan, domin bincike.
“Tabbas ‘yan iska sun kashe basaraken. Amma shi kaɗai aka kashe. A cikin motar sa aka banka masa wuta bayan an kashe shi.
“Kwamishinan ‘Yan Sanda ya je har wurin domin bincike, kuma ina tabbatar maku cewa sai mun kamo waɗanda suka yi kisan an gurfanar da su, an hukunta su daidai laifin da suka aikata.”
Discussion about this post