Aƙalla mutum 486 ne ‘yan bindiga su ka bindige a sassa daban-daban na ƙasar nan, cikin kwanaki 21 na farkon sabuwar shekarar 2022.
Kusan kashi 80 bisa 100 na waɗanda aka bindige ɗin duk an kashe su ne a jihohin Arewa maso Yamma.
Sannan kuma a Jihar Neja ne aka bindige kashi 50 bisa 100 na yawan mutum 486 da aka kashe a Najeriya a cikin kwanakin.
Sai kuma jihar Zamfara, inda aka kashe kusan kashi 50 bisa 100 su ma.
Binciken PREMIUM TIMES ne da kuma ƙididdigar labaran hare-hare da jaridu ke bugawa ya tabbatar da kashe wannan adadin mutane masu tarin yawa.
Gwamna Sani Bello na Jihar Neja ya bayyana cewa an kashe mutum 220 a Jihar Neja tsakanin 1 zuwa 17 Ga Janairun sabuwar shekarar 2022.
Tsakanin makon farko na 2022, an kashe mutum 200 a Zamfara, bakwai a Kaduna, uku a Filato, uku a Akwa Ibom, wasu uku a Ondo.
Waɗannan kashe-kashen sun faru ne kwanaki kaɗan bayan Shugaba Buhari ya ce an inganta tsaro a faɗin ƙasar nan.
Cikin mako na biyu na watan Janairu, an kashe mutane 37. Mutum 18 aka bindige a Filato, 17 a Kebbi, sai Imo, Abuja da kuma mutum ɗai-ɗai.
Cikin mako ma uku an kashe mutum 13, waɗanda su ka haɗa da uku a Kaduna, 1 Ebonyi, huɗu Akwa Ibom, sai Neja mutum 4.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, wato Garba Shehu, ya tabbatar da cewa yanzu an tashi haiƙan wajen kakkaɓe duk wani ɗan bindiga.
Discussion about this post