Al’ummar Ɗansadau da ke cikin Ƙaramar Hukumar Maru sun yi bikin cika watanni biyu da ƙulla yarjejeniya da ‘yan bindiga.
Sun ƙulla yarjejeniyar ce a cikin watan Nuwamba, 2021, tsakanin manoma da makiyaya, cikin har da ‘yan bindiga a yankin gundumar.
Garin Ɗansadau na da tazarar kilomita 100 tsakanin sa da Gusau, babban birnin Jihar Zamfara. Kuma ya na daga sahun gaba na yankin da ya fi fama da farmakin ‘yan bindiga.
Mazauna yankin ba su iya shiga Gusau ko barin Gusau su koma gida ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba.
Baya ga kai wa ƙauyukan yankin hare-hare, ‘yan bindiga kan tare hanyar Ɗansadau zuwa Gusau.
PREMIUM TIMES a shekarar da ta gabata ta buga labarin yadda mahara suka tare hanya, su ka banka wa motar tankin ɗaukar mai wuta, a lokacin kuma jami’an tsaro na yi mata rakiya.
Sun yi haka ne domin su hana kai fetur a garin Ɗansadau. Kuma su ka tare hanya su hana kai kayan masarufi ko kayan abinci a Ɗansadau.
Su na yin haka ne a matsayin ramuwar gayya kan dokar hana sayar wa makiyaya kayan abinci da kayan masarufi da aka kafa a yankin Ɗansadau.
Yadda Aka Ƙulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya Da ‘Yan Bindiga:
Wani basaraken yankin wato Wazirin Ɗansadau mai suna Mustapha Umar, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mutanen yankin sun ƙulla yarjejeniyar ce bayan an shafe shekaru ana hare-hare da kashe-kashe a yankin tsakanin makiyaya da manoma.
Umar ya ƙara da cewa shugaban ‘yan bindigar yankin wato Ali Kachalla ne ya shirya zaman sasantawa, a lokacin da ya aika da tawaga zuwa garin Ɗansadau a cikin Nuwamba.
Ya ce gwamnatin jiha ta amince a yi zaman bayan zaman da ta taɓa yi da mahara bai ƙulla komai ba.
Umar ya ce sun amince da tayin zaman lafiyar da Kachalla ya nemi a yi, saboda surƙuƙin dajin da ke kewaye da Ɗansadau na bai wa mahara mafaka.
Yankin ya yi iyaka da dazukan Katsina, Kaduna, Kebbi da Neja.
“Tsakanin Ɗansadau zuwa Gusau kilomita 97 ne. Amma tsakanin Ɗansadau da Maru, inda can ne hedikwatar ƙaramar hukuma, kilomita 145 ne, kuma hanya ɗaya ce ake bi a je, wadda kuma ita ce ‘yan bindiga ke datsewa.” Inji Wazirin Ɗansadau.
Ya ce mazauna garin da yankunan karkarar sun fahimci cewa ba za su iya jira har sai ranar da gwamnati ta kare su ba, shi ya sa su ka yanke shawarar ƙulla yarjejeniya da ‘yan bindiga, domin su samu zaman lafiya.
“Mun yarda makiyaya su riƙa shiga Ɗansadau su na sayen kayan abinci da kayan buƙatu na masarufi.
“Amma duk makiyayin da ya shiga Ɗansadau ɗauke da makami, to ya kuka da kan sa.”
“A ɓangaren ‘yan bindiga kuwa, sun yarda za su daina kai hare-hare kuma za su daina tare matafiya kan hanyar zuwa Gusau. Kuma za su ƙyale manoma su yi noma har su kwashe amfanin gonar su.
“Kuma ‘yan bindiga su ka amince su sako dukkan mutane da suka kama a yankin Ɗansadau, ba tare da gindaya mana wasu sharuɗɗa ba.”
Ya ce tun daga lokacin mutane suka riƙa karakaina zuwa Gusau ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba.