A asibitin ‘Olives Specialist Hospital’ dake Ado-Ekiti jihar Ekiti ne wata mata mai suna Temitope Ogundipe dake da shekaru 63 ta haifi jariri.
Matar ta samu wannan karuwa duk da ta dara shekarun haihuwa ta hanyar dabaran haihuwa ta zamani wato ‘In Vitro Fertilisation (IVF)’.
IVF dabarace da likitoci ke yin amfani da maniyin namiji da na ita matar da take so ta haihu sai a saka shi a cikin mahaifar ta.
Temitope ta ce a cike take da murna ganin Allah ya azurta ta da da nata na kanta. Ta ce ta dade tana ta neman haihuwa amma bai yiwu ba.
” Babu irin asibiti da kwayar maganin da ban sha ba domin in samu haihuwa amma bai samu ba. Har IVF din nan da ake yi duk na yi amma dan bai zauna a ciki na ba.
Temitope ta yi godiya ga likitan asibitin Adebayo Adeniyi wanda ya tsaya tsayin daka har Allah ya kai ta ga samun wannan dan.
Ta yi kira ga duk mata masu neman haihuwa da kada su karaya domin idan har Allah zai bata da a yanzu suma Allah zai yi musu.
“Ina kira ga matan dake fama da irin wannan matsala su nemi taimako wajen kwararrun likitoci ko zasu kai ga harawa.
Likitan asibitin Adeniyi ya mika godiyarsa ga Allah kan nasarar da suka samu wajen ganin an yi nasara har Temitope ta haihu.
Adeniyi ya yi kira ga gwamnati da ta rage farashin IVF domin talakawa masu neman haihuwa su iya samu.
Ya kuma ce rashin haihuwa babu dadi da hakan ke sa ka kwanciyar hankali a zukatan mutane musamman wadanda ke neman sa ruwa a jallo
A dalilin haka ya yi kira ga gwamnati da ta saka IVF cikin tsarin inshorar lafiya domin kowa da kowa ya samu.