Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana abin da ya sha yi wa alwashin cewa nan ba da daɗewa ba matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan za ta zama tarihi.
Buhari ya yi bayanin ne lokacin da shugaban mabiya Ɗariƙar Tijjaniya na Duniya, Sheikh Tidjani Ali Bin Araby ya kai masa ziyara a fadar sa, a Abuja.
Arabi ya samu rakiyar Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da babban malamin addinin Musulunci a Ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Bauchi.
A cikin wata sanarwa, Gwamnatin Tarayya ta ce ta na sane da ƙalubalen tsaro a ƙasar nan, kuma ta na bakin ƙoƙarin ta.
Buhari ya ce idan za a ɗora gwamnatin sa a sikelin tsaro, to kamata ya yi a fara auna gejin matsalar tsaro a ƙasar kafin ya hau mulki a 2015, sannan a auna da irin nasarorin tsaro da ingancin sa wanda aka samu daga 2015 zuwa yau.
Buhari ya buga misali da irin nasarorin da Gwmnatin sa ta samu a yankin Arewa maso Gabas da Kudu masu Kudu.
Daga nan ya roƙi ‘yan Najeriya su taya gwamnati magance matsalar tsaro a ƙasar nan, ta hanyar sa-ido da taimaka wa gwamnati.
Premium Times Hausa ta buga kamalan da Buhari ya saboda shi ma malejin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci sun kara cillawa sama.
Najeriya na daya daga cikin kasashen da su ka fi fama da marasa aiki da zauna-gari-banza a duniya.