Tsohon Gwamnan Jihar Barno Ali Modu Sheriff ya ce babu mahalukin da ya yi wa jam’iyyar APC aiki tuƙuru, tun farkon kafuwar ta, kamar shi.
Ya ce a matsayin sa na ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka kafa APC, babu abin da ke cikin sa da zuciyar sa kamar ganin cewa jam’iyyar ta bunƙasa sosai.
Sheriff ya yi wannan bayani a wani taron manema labarai, ranar Juma’a, a Abuja.
Sheriff wanda tsohon sanata ne kafin ya mulki Barno, ya bayyana cewa zai fito takarar shugabancin APC na ƙasa baki ɗaya.
Duk da cewa jam’iyyar ba ta bayyana shiyyar da za ta damƙa wa takarar shugabancin jam’iyyar ba, amma dai za a yi Taron Gangamin Jam’iyya a ranar 26 Ga Fabrairu.
Sheriff wanda har Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa ya taba riƙewa, ya ce a yanzu ya na so ne ya fito takarar shugabancin APC, idan aka damƙa shugabancin APC ɗin ga ‘yan yankin Arewa maso Gabas.
Sannan kuma ya ce tuni har ma ya yi nisa da tuntubar manya, dangane da yadda za a yi wa APC garambawul domin fuskantar ƙalubalen da ka iya yi wa APC karan-tsaye, bayan kammala wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari kan mulki.
Modu Sheriff ya ce gogewar da ya samu a shugabancin PDP, za ta zama wata ‘ribar-ƙafa’ ce wurin sa idan ya kama ragamar shugabancin APC.
“Kai ni fa dama ban taɓa yankar katin zama ɗan PDP ba a rayuwa ta. Amma dai a haka su ka ba ni shugabancin jam’iyyar, wanda kuma gogewar da na yi kan riƙon PDP zai ƙara min tasiri idan na zama shugaban APC, kuma ita ma APC ɗin za ta ƙara karsashi.
“Da ni aka fara kafa APC, kuma ina cikin mutane shida da su ka fara zaman kafa jam’iyyar. Ni ne Shuagaban Kwamitin Amintattun APC na farko.” Inji Modu Sheriff.
Ya ce idan aka zaɓe shi shuagabancin APC, zai nunka ƙoƙarin da ya wa PDP har nunki goma.
Sheriff ya taɓa cewa a rubuta a ajiye, APC sai ta yi mulkin Najeriya tsawon shekaru 40 ko 50.