• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare

    2015-2023: ‘Na yi sukuwa ta lafiya, na kai zamiya lafiya’ – Buhari

    BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

    Tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje, Daga Jaafar Jaafar

    Ba zan jira Litinin ba, tun Lahadi zan mika mulki ga Abba Gida-Gida in kama gaba na – Ganduje

    RANTSAR DA TINUBU: Kotun Koli ta yi watsi da karar rashin cancantar Tinubu shiga zaɓen 2023

    RANAR RANTSAR DA TINUBU: Za mu hana makiyaya karakaina da shanu a cikin Abuja – Shugaban Miyetti Allah

    An Karrama gidan Jaridar PREMIUM TIMES da kyauta mafi daukaka a aikin Jarida na kasar Amurka

    BA DA MU BA, TAYA ƁERA ƁARI: PREMIUM TIMES ta nesanta kan ta daga ƙungiyar da ta jona sunan ta a shirya taron karrama wasu mutane

    KIRAN RUWA: ‘Ka wa Allah ka ɗaga mana kafa, kada ka kwace mana filayen mu har 9 da ka kunno kai a kan su – Makarfi ga El-Rufai

    ‘Ni da Wike kaman ‘Yan biyu ne, muna tsage gaskiya komai dacin ta’ – El-Rufai

    SABODA TIWITA: Sanatocin PDP sun fice daga Zauren Majalisar Dattawa

    Zaɓaɓɓun Sanatocin Arewa ta Tsakiya sun nemi a ba su Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ko a-yi-ta-ta-ƙare

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

MAJALISAR TARAYYA A 2021: Tasirin ‘Yan Gaske, Takidin ‘Yan Gangan, Tuggun ‘Yan Gargar

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
January 17, 2022
in Rahotanni
0
KASAFIN 2022: Sanata Lawan ya damu da wawakeken giɓin da aka samu

Yayin da aka fara zaman Majalisar Tarayya na sabuwar shekarar 2021 cikin watan Fabrairu a lokacin, babban abin da kowane ɗan Najeriya mai gaganiyar neman yadda zai ciyar kan sa ya riƙa tunani, shi ne yadda Mambobin Majalisar Tarayya za su fito da dokokin gaggawa domin gwamnati ta gaggauta rage wa jama’a raɗaɗin ƙuncin rayuwa sanadiyyar ɓarkewar cutar korona.

To amma idan ka ɗebe batun kasafin kuɗi da kuma yawan amince wa Shugaba Muhammadu Buhari ya ciwo bashi, babu wani tasirin kirki da su ka yi domin rage wa jama’a zafin ƙuncin rayuwar dalilin annobar korona.

Abin takaici, sai Majalisar Tarayya da gwamnatin tarayya su ka fara cacar-baki’ a kan ma’aikata 774,000 da za a ɗauka domin yi wa gwamnati aikin leburancin, shirin da Ma’aikatar Ƙwadago za ta kula a ƙarƙashin ta.

Haka nan kuma sai ‘yajalisa su ka kasa tambayar kan hanzarin Buhari na neman amincewa ya riƙa biyan mutum miliyan 40 Naira 5,000 da ya ce zai riƙa yi idan an cire tallafin fetur.

A taƙaice dai an samu ci gaba da tasiri cikin Majalisar Tarayya a 2021, kuma an sha fama da takidin ‘yan gangan da kuma tuggun ‘yan gargar.

Majalisar Tarayya A 2021: Tasirin ‘Yan Gaske:

Cikin shekarar 2021 ne Majalisar Tarayya ta karya ƙofi da makarun da aka yi wa Ƙudirin Gyaran Dokar Man Fetur, wanda ya shafe shekaru 17 a majalisar tarayya ana ina-ni-ka-ina-ni-ka-aje da shi. Yanzu dai Shugaba Muhammadu Buhari tuni ya sa wa ƙudirin hannu ya zama doka.

Abu na biyu kuma shi ne Ƙudirin Dokar Canjin Yanayi wanda Majalisa ta miƙa, shi ma Buhari ya sa masa hannu a cikin 2021 ya zama doka.

Ƙudirin wanda Honorabul Samuel Onigbo ya gabatar, ya sha fama da jijjige-jijjige, kauce-kauce da kakkaɓe-kakkaɓe a baya.

Sasanta Tankiya Da Saɓani A Gwamnati:

Majalisar Tarayya ta yi abin ƙwarai wajen sasanta rashin jituwa tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyi.

Ta sasanta Gwamnatin Tarayya Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), wanda Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya jagoranta.

Haka cikin Disamba Gbajabiamila ya shugabanci zaman sasanci tsakanin Najeriya da UAE domin ɗinke ɓarakar da ta tashi kan jigilar fasinjoji tsakanin ƙasashen biyu.

Gano Kuɗaɗen Da Ma’aikatu Suka Karkatas:

Cikin 2021, Majalisar Tarayya ta yi aƙalla zama 10 da Ministar Kuɗaɗe Zainab Ahmed, Ministan Shari’a Abubakar Malami, Akanta Janar na Tarayya Mai Binciken Kuɗaɗe, Shuagan EFCC Abdulrashid Bawa da wasu shugabannin hukumomi.

Majalisa ta gano yadda Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da Cibiyoyin Gwamnantin Tarayya da Hukumomi ba su maida kuɗaɗen da su ka rage a ƙarshen shekara, tsawon shekaru da dama.

Wasu ma’aikatun ma har yanzu ba su bin tsarin ajiyar kuɗaɗen gwamnati a Asusun Bai-ɗaya (TSA).

Majalisa ta gano kuma ta riƙa kafa kwamitin bincike. Sai dai har yanzu kwamiti bai kammala ba, tsawon watanni shida kenan, saboda yanzu bincike ya koma cikin bankunan da ake kimshe kuɗaɗen.

Majalisar Tarayya A 2021: Takidin ‘Yan Gangan Da Tuggun ‘Yan Gargar:

Lokacin da aka yi hayaniyar rufe shafin Tiwita dai Majalisar Tarayya na hutu. Wasu mambobin musamman ‘yan adawa sun riƙa kartar ƙasa su na cewa idan su ka koma majalisa da ga hutu, za su tada ƙayar baya, sai gwamnatin tarayya ta buɗe Tiwita.

Ana komawa sai Kakakin Majalisar Tarayya Gbajabiamila ya shiga, ya fita ya yi biji-biji da batun. A ƙarshe dai ya kafa kwamitin bincike. Kwamiti kuma ya goyi bayan kulle Tiwita.

Majalisar Tarayya A 2021: Yawan Mutuwar ‘Yan Majalisa Laifin Masu Damun Su Da Maula Ne -Ben Kalu

Shekarar 2021 ta ci rayukan wasu ‘Yan Majalisar Tarayya. Mutuwa ta ɗauki ran Ossy Prestige, inda ta bi shi har cikin asibitin ƙasar Jamus ta ɗauki ran sa a ranar 9 Ga Fabrairu, 2021.

Cikin watan Maris kuwa rayukan ‘yan majalisa biyu mutuwa ta ɗauka. Akwai Haruna Maitala, wanda ya rasa ran sa sakamakon hatsarin mota, tsakanin Keffi zuwa Abuja, kan hanyar sa ta komawa Abuja daga Jos. Sai Hassan Kila wanda ya rasu a Babban Asibitin Tarayya na Abuja.

Cikin watan Afrilu Adebayo Omolefe ya rasu a Asibitin Gwamnonin Tarayya (FMC) da ke Owo, Jihar Ondo.

Sai da kuma Kakakin Yaɗa Labaran Majalisar Tarayya, Ben Kalu, ɗan APC daga Jihar Abia, ya danganta mutuwar ta su da yawan damun su da ake yi da bani-bani, roƙon kuɗi da maula, musamman daga jama’ar mazaɓun su.

Majalisar Tarayya A 2021: Yunƙurin Ƙaƙaba Wa Jaridu Takunkumi Bai Yi Nasara Ba:

Haka kawai wani Segun Odebunmi, ɗan APC daga Jihar Oyo, wanda ko ‘bihim’ bai sani ba a aikin jarida, ya bijiro da ƙudirori biyu domin kafa wa jaridu da soshiyal midiya takunkumi.

Jaridu da Ƙungiyoyin Kare Marasa Karfi kuwa su ka riƙa ragargazar yunƙurin na su, har dai a ƙarshe tilas aka janye ƙudirorin biyu, ɗaya na NBC ɗaya kuma na NPC.

Cikin 2021 an sha gwagwarmaya da Ƙudirin Dokar Fetur, to kuma an ga yadda a ƙarshe aka yi wurgi da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe.

Shin ko ya Majalisar Tarayya za ta kasance a 2022? Muna jira, muna ji, muna gani, muna kuma saurare.

Tags: AbujaHausaLabaraiMajalisaNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

NASIHAR BUHARI GA ‘YAN NAJERIYA: Ku riƙa yi mana adalci idan ku na tattauna matsalar tsaron ƙasar nan

Next Post

ZAƁEN CIKE GURBI: INEC za ta yi zaɓuɓɓukan cike gurabe a jihohi 4 a ranar 26 Ga Fabrairu

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

ZAƁEN CIKE GURBI: INEC za ta yi zaɓuɓɓukan cike gurabe a jihohi 4 a ranar 26 Ga Fabrairu

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Ganduje ya bar wa Kano bashin Naira biliyan 241, Abba ya ce zai bi ya gano hanyoyin da aka ciwo bashin
  • Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare
  • JAWABIN BANKWANA: Ba a taɓa gwagwagwar zaɓen shugaban ƙasa kamar na 2023 ba – Buhari
  • JIGAWA A HANNUN BADARU: Yadda shekaru takwas na mulkin APC ya kasa rage katutun talauci da fatara
  • BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.