Hukumar NCDC ta bayyana cewa cutar kwalera ta yi ajalin mutum 3,604 a shekarar 2021 a Najeriya.
Alkaluman yaduwar cutar na mako 52 da hukumar ta fitar ya nuna cewa shekarar 2021 itace shekarar da cutar ta fi yaduwa da kisan mutane a kasar nan.
Hakan ya faru ne saboda yadda gwamnati ta fi mai da hankali ta wajen yaki da cutar korona.
A shekarar 2021 mutum 111,662 ne ake zaton sun kamu da cutar a kasar nan.
Yaduwar cutar
A shekarar 2021 cutar ta bayyana a kananan hukumomi 435 a jihohi 33 a Najeriya.
Hukumar ta ce yankin Arewa ce yankin da ta fi fama da yaduwar cutar a shekarar 2021.
Jihohin Bauchi mutum 19,558, Jigawa mutum 15,141 da Zamfara mutum 11,931 na daga cikin jihohin da suka fi fama da yaduwar cutar a Arewacin Najeriya.
Abubuwa 10 dake haddasa barkewar cutar a kasar nan
1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.
2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.
3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.
4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.
5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.
6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.
7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.
8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.
9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.
10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.