Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bada sammacin kamo tsohuwar Ministar Fetur Diezani Allison-Madueke, wadda ake tuhuma kan zargin satar maƙudan kuɗaɗe a lokacin da ya ke minista, lokacin mulkin Goodluck Jonathan, 2010-2015.
Wannan sammacin umarnin kamo Diezani dai shi ne na biyu, kuma yanzu haka ta na zaune a Landan tun bayan ficewar ta daga Najeriya cikin 2015.
A ranar 4 Ga Disamba, 2018 ne Mai Shari’a Valentine Ashi na Babbar Kotun Tarayya, Abuja ya bayar da sammacin a kamo Diezani. Ya bayar da umarnin ne ga Hukumar EFCC, ‘Yan Sanda da SSS a lokacin.
Daga baya Valentine Ashi ya mutu, inda EFCC ta sake maida ƙarar Babbar Kotun Tarayya, ya gabatar da tuhuma 23 duk ta zargin satar maƙudan kuɗaɗe, tare da neman a kamo ta domin ta fuskanci shari’a a Najeriya.
A ranar 24 Ga Yuli, 2020 Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta aika wa Diezani Allison-Madueke sammacin neman ta bayyana a kotu domin amsa tuhuma. Amma shiru ka ke ji.
Daga nan EFCC ta nemi kotu ta ba ta sammacin umarnin kamo Diezani a Landan, wanda kotun ba ta yi hakan ba a lokacin. Ta ce sammacin da ta bayar na ta bayyana ya wadatar.
A yanzu Mai Shari’a Bolaji Olajuwon wanda ya karɓi tuhumar daga Mai Shari’a Ujukwu ne bayar da sammacin umarnin kamo Diezani ga lauyan EFCC, Farouk Abdullahi.
Daga cikin maƙudan kuɗaɗen da ake tuhumar Diezani da sata, har da wasu dala miliyan 39.7 da kuma naira biliyan 3.32 da sauran maƙudan kuɗaɗe.
Discussion about this post