Kotun majistare dake Iganda jihar Legas ta gurfanar da wata mata mai shekara 63 a dalilin fasa kwalban giya akan kawunsa da yayi ya ji masa rauni a kai.
Ɗan sandan da ya kawo ƙara gaban kuliya ASP Clement Okuiomose ya ce ɗan wannan mata mai suna Godonu ya aikata wannan abu ne ranar 24 ga Janairu a gida dake lamba 45 Awuse Badagry.
Okuiomose ya ce gardama ce ta kaure tsakanin Godonu da kawunsa daga nan sai suntumi ya kwalban giya ya fasa akan kawunsa ya ji masa rauni.
Ya ce bayan an kai karar abinda ya faru a ofishin ƴan sanda sai mahaifiyar Godonu ta ce wa Godonu ya arce kada ƴan sanda su kama shi.
“Da ƴan sanda ba su iya gano inda yake ba sai muka kamo mahaifiyarsa muka kaita kotu domin yanke mata hukunci a madadin ɗanta.
Mahaifiyar Godonu ta musanta aikata laifi a gaban alkali. Sai dai hakan bai hana alkalin ɗaure ta ba ko kuma ta biya belin naira 50,000 ba.
Alkalin Fadahunsi Adefioye ya bada belin mahaifiyar akan Naira 50,000 tare da gabatar da shaida daya.
Za a cigaba da shari’a ranar 24 ga Fabrairu.