Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana cewa gwamnati ta yi wa mutane akalla miliyan 70 rigakafin annobar Korona a kasar.
Shugaba Biden ya yi kira ga mutane musamman wadanda ya kamata su yi rigakafin cutar da su gaggauta yin allurar domin samun kariya daga kamuwa da cutar.
Biden ya fadi haka ranar Talata a taron da ya yi da manema labarai da masu bashi shawara kan dakile yaduwar cutar korona a fadar shugaban ƙasa wato ‘White House’.
Zuwa yanzu Kashi 60% na mutanen da ya kamata su yi allurar rigakafin korona a kasar sun yi allurar rigakafin cutar sannan kashi daya bisa uku daga cikinsu kuma sun yi allurar rigakafin inganta kariya daga kamuwa da cutar a kasar.
“Yin rigakafi zai taimaka wa mutane wajen samun kariya daga kamuwa da cutar da kuma hana mutane galabaita ko kuma ya kai ga mutuwa ma a dalilin cutar.
“Na San cewa duk mun gaji da yaduwar cutar amma gwamnati ta tanadi isassun maganin rigakafin cutar wanda idan muka ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar za mu samu nasara wajen dakile yaduwar cutar.
Ya ce yin rigakafin korona kyauta ake yi a wuraren yin allurar 90,000 a kasan.
“Gwamnati ta Kara yawan ma’aikatan da za su rika yi wa mutane allurar rigakafin, ta Kara yawan wuraren da ake yin rigakafin sannan ta kara yawan lokacin da jami’an lafiya za su rika aiki domin ganin an dakile yaduwar cutar.
“Sannan nan ba da dadewa ba gwamnati za ta karo ruwan maganin rigakafin har miliyan 20 na kamfanin Pfizer da Paxlovid.
Ya kuma kara da cewa gwamnati ta ware Dala tiriliyan 1.9 domin tallafawa makarantun ƙasar duk da tuni wasu makarantun sun fara koyar da ɗaliban su ta yanar gizo.
Discussion about this post