Uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari, A’isha Buhari ta shiga cikin sahun dimbin ‘yan Najeriya masu kiran a zartas da hukuncin kisa a kan malamin Hanifah Abubakar, wanda ya kashe ta bayan ya yi garkuwa da ita.
A’isha ta nuna wannan goyon bayan ta hanyar watsa wani bidiyo na Sheikh Abdallah Gadon Ƙaya da ke Kano.
A cikin ɗan guntun bidiyon, Malam Gadon Ƙaya ya yi kira ga hukuma da masu kare haƙƙin jama’a da ‘yan jarida su takura su tabbatar da lallai an zartas da hukuncin kisa kan wanda ya kashe yarinyar ‘yar shekara biyar da haihuwa.
“Muna so a kashe shi kamar yadda ya kashe ta, tunda ran sa bai fi ran ta ba. Kuma a gaban jama’a mu ke so a kashe shi, don ya zama darasi ga saura.” Inji Gadon Ƙaya.
A’isha Buhari a ƙasan wannan bidoyo, ta rubuta goyon bayan ta kasar haka.
“Muna goyon bayan hukuncin Malam.”
Premium Times ta bada labarin yadda hasalallun matasa su ka banka wa makarantar malamin wuta, inda a can ne ya binne gawar ta, bayan ya kashe ta.
Hasalallu sun banka makarantar da aka binne gawar Hanifah wuta.
Wasu hasalallun matasa sun banka wa makarantar da aka binne gawar marigayiya Hanifah Abubakar wuta.
Malami kuma mai makarantar ne ya binne ta a ciki, bayan ya kashe ta ta hanyar sa mata samandagarin ɓera a cikin abinci, sannan aka daddatsa jikin ta kafin a binne ta.
Makarantar mai suna Noble Kids Comprehensive College, ta na cikin unguwar Kwanar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nasarawa a cikin Kano.
Malamin mai suna Abubakar Tanko ne ya yi garkuwa da ita tun a ranar 2 Ga Disamba, 2021.
Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta kama Tanko bayan ya rigaya ya karɓi kuɗin fansa, kuma ya kashe yarinyar.
Bayan kama shi, ‘yan sanda sun kai shi ya nuna masu inda ya gina rami ya binne gawar yarinyar. Daga nan kuma gwamnatin Jihar Kano ta rufe makarantar.
Kakakin ‘Yan Sandan Kano Abdullahi Koyawa ya faɗa a ranar Litinin cewa cikin dare a ranar Lahadi ne matasa su ka banka wa makarantar wuta.
Sai dai ya ce har yanzu ba a kama kowa ba tukunna. Babu wanda ya ji ciwo, amma wani sashe na makarantar ya ƙone.
Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa jami’an SSS da ‘Yan Sanda, saboda ƙoƙarin da suka yi har suka kama wanda ya kashe yarinyar.
Kisan Hanifah: Minista Pantami Ya Je Ta’aziyya Gidan Iyayen Ta:
A ranar Lahadi ce kuma aka nuno motunan makamin addinin Musulunci, kuma Ministan Sadarwar Zamani, Isa Pantami ya kai ziyara gidan iyayen marigayiya Hanifah a Kano.
Haka shi ma Sanata Ibrahim Shekarau, wanda tsohon Gwamnan Kano ne, kuma Sanatan da ke wakiltar yankin da Hanifah ya fito, ya sha alwashin bin shari’ar har sai an yanke hukunci kuma an zartar da hukunci kan wanda ya kashe Hanifah.
Discussion about this post