Kungiyar kiristoci rashen jihar Kaduna, CAN ta yaba namijin ƙoƙarin da rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta yi wajen ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su tare da kama masu garkuwa da mutane biyu a jihar.
Shugaban hukumar Joseph Hayab ya sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai a jihar.
Hayab ya ce wannan ci gaba da aka samu ya yi wa mutane ɗaɗin gaske.
“Wannan ci gaba da aka samu na daga cikin bukatun da mazauna jihar Kaduna ke yin addu’o’i Allah ya kawo saukin su. Fatan mu shine Allah ya sa wannan aiki da jami’an tsaro suka fara zai ci gaba har sai an ga karshen miyagun mutane irin haka a jihar.
“Wannan aiki da rundunar ta fara musamman a ranar farko ta shekaran 2022 sannan fatan mu shine aiyukkan da rundunar ta fara zai taimaka wajen dawo da sauran mutanen dake hannun masu garkuwa da mutane gidajen su lafiya.
Hayab ya ce miyagun aiyukkan da mahara ke aikatawa ya takura wa kwanciyar hankali da zaman lafiya fiya a jihar.
“Ya zama dole a ɗauki matakan da za su taimaka wajen hana maharan ci gaba da muzguna wa mutane a jihar.
Ya ce kungiyar CAN za ta ci gaba da hada hannu da jami’an tsaro domin ganin bayan mahara a jihar.
“Samar da tsaro hakki ne da ya rataya akan kowa a jihar Kaduna.
Discussion about this post