Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bashi da ɗan takara ɗaya da zuciyarsa ta raja’a akan shi ya gaje shi.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a hira da ya yi da Talbijin din Channels TV a Abuja ranar Laraba.
” Ba ni da wanda na ke so karara ya gaje ni a 2023, idan ma akwai toh zan barshi a can cikin zuciyata kawai domin idan na faɗi kila gobe a neme shi a rasa.
Wa’adin mulkin Buhari zai kare ni a cikin shekarar 2023, wannan yasa tun daga yanzu masu sha’awar maye gurbin sa ya san ya sauka suka fara daura niyya.
A cikin kwanakin nan, kungiyoyi daban-daban sun rika fitowa suna tallata mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, cewa shine ya fi dacewa ya yi takarar kujerar shugaban Kasa idan Buhari ya kammala wa’adin sa.
Sai dai kuma shima jigon jam’iyyar, Bola Tinubu ya dade yana nuna zai fito takarar shugaban kasa a 2023. Sai dai kuma dukkan su basu bayyana ra’ayoyin su ba tukunna.
Haka kuma shima tshon shugaban kasa, Goodluck Jonathan akwai waɗanda suke ganin akwai yiwuwar zai canja jam’iyya ya dawo APC domin ta bashi takarar shugaban kasa.
Har yanzu dai babu wanda ya fito daga cikin su ya bayyana kararar cewa yana son fitowa takarar shugaban kasa a 2023.
Koma dai wanene idan lokaci yayi zamu gani.