Akalla mutum 9 ne aka kashe sannan wasu mazauna da dama sun gudu daga gidajen su a dalilin harin da ‘yan bindiga suka kai ranar Lahadi a karamar hukumar Tsafe.
Wani mazaunin Tsafe Salisu Sabo ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan sun afka kauyukan Magazawa, Kajera, Unguwar Dan Halima, Unguwar Rogo, Unguwar Ango, Kurar Mota da Kauyen Kane duk a karamar hukumar Tsafe ranar Lahadi.
“Maharan sun fi yin barna a kauyen Magazawa domin sun kashe mutum 7 a kauyen. Ba mu da labarin ko maharan sun kashe mutane a sauran kauyukan amma mutane da dama a sauran kauyukan duk sun arce daga gidajen su zuwa garin Tsafe.
Mustapha Sani ya ce harin da ‘yan bindigan suka kai ya ritsa da wasu ‘yan uwansa da suka je bikini da daurin aure a Magazawa.
Sani ya ce an kashe mutum 7 a kauyen Magazawa sannan mutum biyu a Unguwar Kane.
Sai dai kuma Jami’an tsaro sun fatattaki ‘yan bindigan a kauyen Yandoton Daji.
Kungiyar ‘yan sa kai da ‘yan sanda sun fatattaki ‘yan bindigan da suka kai farmaki kauyen Yandoton Daji.
‘Yan bindigan sun shiga kauyen da karfe 12 na rana amma ‘yan sa kan suka fatattake su.
‘Yan indigan sun gudu zuwa dajin Munhaye bayan da suka ga an sha karfin su.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar bata ce komai ba.
Discussion about this post