Da safiyar litinin ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutum 7 mazauna kauyukan Margai da Gaddace a karamar hukumar Kebbe, jihar Sokoto.
Karamar hukumar Kebbe gari ne dake Kudancin jihar Sokoto kuma garin bata cika samun barazanar hare-haren ‘yan bindiga kamar yadda ake fama da su a garuruwan dake Arewacin jihar ba.
Wani mazaunin garin Kebbe da baya so a fadi sunan sa saboda tsaro ya ce ‘yan bindigan sun fara kai farmaki kauyen Margai ne kafin suka zarce kauyen Gaddace.
Ya ce ‘yan bindigan sun dira kauyen da karfe dayan dare ne sannan suka fara sassare kofofin gidajen mutane da shaguna suka fara kwashe kayan jama’a.
“Da sun ga mutane za su zo wurin su sai su rika harbi a sama domin tsorata su sai kowa ya arce a koma da baya.
Ya ce sun sace mutum uku a wannan kauyen da ciki akwai wani mahaifi da dansa.
Sannan kuma a kauyen Gaddace wani mazaunin garin ya ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 4.
Ya ce babu ran da aka rasa amma ‘yan bindigan sun saci kaya da dabbobin jama’a.
Kakakin rundunar’yan sandan jihar Sanusi Abubakar ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES cewa bashi da masaniyar abin da ya faru a wadannan kauyuka da aka ce an far musu.
Discussion about this post